Majalisar Wakilai ta gayyaci karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri da takwaransa mai kula da iskar Gas, Ekperikpe Ekpo game da matsalar karancin man da ake fuskanta a kasar nan.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri da dan majalisa, Umar Ajilo, ya gabatar, inda ya bayyana damuwa game ci gaba da samun dogayen layuka a gidajen man da ke fadin kasar nan.
- Gwamnonin Arewa Sun Nuna Ƙwarin Gwiwarsu Na Samar Da Kyakkyawar Makomar Yankin
- JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
Kazalika, majalisar ta gayyaci shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, a kan matsalar karancin man fetur.
Majalisar na sa ran ministocin da shugaban kamfanin NNPCL su yi mata bayani game da asalin dalilan da suka haddasa karancin man da kuma matakan da za a dauka wajen shawo kan matsalar.
Saidai ba a tsayar da ranar ganawar ba.
Yanzu haka dai ana ci ga a da samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen man a fadin kasar nan.
‘Yan Nijeriya da dama ja ci gaba da kokawa kan yadda suke sayen man fetur da tsada, inda wasu gidajen mai ciki har da NNPC ke sayar da fetur daga Naira 1000 zuwa sama kan kowace lita.
Hakan ya sanya an fara samun karancin ababen hawa a kan tituna, lamarin da ya fara haifar da tsaiko ga al’amuran yau da kullum.