Tsohon mawakin soyayya a masana’antar Kannywood wanda ya yi shura a fagen wakokin soyayya a shekarun da suka gabata, Ahmed Mahmud Abdulkadir ko kuma Mahmud Nagudu kamar yadda aka fi saninsa ya karyata wadanda suka ce ya bayyana wakokin soyayya a matsayin haramun, inda ya tabbatar da cewar wasu dalilai ne suka sa ya daina wakokin soyayya ba don suna da haramci ba kamar yadda wasu suke fadi.
Mahmud a wata hira da ya yi da jaruma Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna Gabon’s Room Talk Show ya yi karin haske a kan wasu daga cikin dalilan da suka janyo ya daina yin wakokin soyayya da aka sanshi dasu a baya,wanda daga ciki akwai karewar basira a wannan fanni na wakokin soyayya kamar yadda ya bayyana.
- Sakataren Kudi Na Ƙungiyar Ɗalibai Shiyya Ta Ɗaya Ya Nemi A Shiga Zanga-zanga
- In Dai Ina Raye, Ba Ni Da Wani Aiki Da Ya Wuce Buga Littattafai – Gidan Dabino
Da farko dai babu inda nace waka haramun ne hasali ma har yanzu ina yin wakoki sai dai ba na soyayya ba kamar yadda aka fi sani na dasu, domin kuwa yanzu shekaruna sun ja kuma ayyuka sun kara yi mani yawa,sannan kuma ina ganin kamar basira ta ta kare a wannan fanni na wakokin soyayya,don ba zai yiwu ace kullum babu abin da zaka dinga fadi a waka ba illa kalmar so kawai, hakan yasa nike ganin kamar babu wani abu wanda na sani a soyayya da ban bayyana shi a cikin wakokin da nayi a baya ba, in ji Mahmud.
Ya ci gaba da cewar yanzu da nake wakoki na yabon Manzon Allah (S A W) akwai bukatar in samu ilimi dangane da wannan Manzo na Allah ba kawai in dinga rera kalaman da suka burge ni ba,amma ita wakar soyayya zaka iya saka duk wani abu da ya zo maka a rayuwa ko kuma ka sani dangane da soyayya a cikin wakokinka ka baiwa mutane kuma a yaba maka ba kamar bege ba.
Da yake amsa tambaya a kan irin sana’ar da yake yi yanzu bayan barin wakokin Kannywood sai Mahmud ya ce kasuwanci yake yi a yanzu ko kuma buga buga kamar yadda bahaushe yake fadi,sannan kuma maganar barin masana’antar Kannywood wannan ba gaskiya bane domin kuwa har yanzu yana abin arziki da masu shirya fina finai da saurnan jarumai a masana’antar ta Kannywood.
Da yake magana a kan matsalolin da yake tunanin sun yi wa masana’antar Kannywood katutu da kuma hanyoyin da zaa bi wajen magance su Mahmud ya ce, babbar matsalar wannan masana’antar ba wani abu ba ne illa rashin kofa ma’ana duk wani wanda yake son shigowa zai ita shigowa ba tareda an san ya shigo ba balantana a tambayeshi wanene shi kokuma daga ina ya fito.
Amma matukar za a dauki mataki a kan irin wadannan mutane masu yi wa Kannywood shigar kutse a dinga tantance su, a bincikesu daga ina suka fito minene sana’oinsu kafin shigowa Kannywood da sauran tambayoyi kafin a basu damar shigowa kokuma mallakar shaidar zama ‘ya’yan Kannywood to za a samu saukin shigowar wadanda suke da karancin tarbiyya da zasu janyowa masana’antar zagi kokuma bacin suna a wajen al’umma.
Dangane da nasarorin da Mahmud ya samu a Kannywood kuwa, tsohon mawakin ya bayyana dimbin nasarorin da ya samu da suka hada da haduwa da manya kuma nagartattun mutane da kuma sauran arzika,daukaka da kuma tarin masoya da yace Allah ya bashi a tsawon shekarun da ya kwashe a masana’antar.