ADO AHMAD GIDAN DABINO, mashahurin marubuci ne kuma har ila yau tauraron da yake haskawa a fagen fina-finai. Wakiliyarmu BUSHIRA A NAKURA ta yi tattaunawa ta musamman tare da shi kwanan baya a Kano. Ga yadda ta kaya a tsakaninsu:
Salam alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko yaya tarihinka a takaice?
Sunana Ado Ahmad Gidan Dabino MON. An haife ni a ranar daya ga watan daya shekar 1964 a Garin Dan Bagina na Karamar Hukumar Dawakin Kudu, amma an yaye ni a Zangon Bare-bari.
- Masana Sun Bayyana Matsalolin Fina-finan Hausa Da Hanyoyin Inganta Su
- Saudiyya Ta Ba Nijeriya Kyautar Tan 50 Na Dabino
A nan na girma har na fara karatun Allo da na Islamiyya a makarantar Malam Rabiu a nan cikin Zangon Bare-bari, daga nan kuma na je Islamiyya ta Malam Ibrahim a nan ‘yan Mota kusa da gidan Sheikh Malam Tijjani na ‘yan Mota Allah ya jikansa. Lokacin da nake karami ban yi karatun Boko ba sai da na girma na kai shekaru 20 sannan na kai kaina Masallaci Adult Ebening Classes na shekara biyu, sannan na tafi GSS Warure na shekara biyu, ita ma tana karkashin hukumar yada ilmin manya ne watau Agency for Mass Education. Na shekara biyu a karamar Sakandare, sannan na shekara biyu a babbar sakandare, watau a shekara shida na yi firamare da sakandare gaba daya. Daga nan na cigaba da harkokin rubutu ban koma makaranta sai a 2005 zuwa 2006 na je na karanta Professional Diploma in Mass Communication. Haka kuma na yi kwasa-kwasai kamar na koyon aikin kafinta, da kuma koyar da makafi watau Special Education, mun koyi ilimin makafi, don mu koyar da makafi da sauran kwasa-kwasai da suka shafi rubutu. Ina da mata daya da ‘ya’ya shida.
Kana yin sana’a ne ko kuma aikin gwamnati kake yi ko kasuwanci?
Eh to, farko kafin na shiga harkar rubutu na yi sana’o’i da yawa. Na yi harkar sayar da huluna. Na kan saya na sayar daga garuruwa mabambanta, duk inda ake sayar da hula a Arewacin Nijeriya na je zamanin da nake harkar. To na yi irin wadannan abubuwa, daga kuma harkar rubutu ta zo ta zama ita nake yi, ina bugawa ina saidawa. Ma’ana littafaina da kuma na mutane wadanda suke bayarwa a buga musu daga gida har wajen Nijeriya kamar kasar Nijar, China duka muna da wadanda muke bugawa littattafai da kuma cikin gida duka Nijeriya babu inda ba ma buga littatafan mutane. Wanda ya hada da na koyarwa a makarantu, na labarai, harkar sauran ilmummuka duka muna wallafawa. Don haka yanzu aikina shi ne mawallafi da kuma kamfanin wallafa da dab’i kuma ina shirya fim, ina bayar da umarni kuma ina fitowa a matsayin dan wasa.
Wacce shekara ka fara rubutu?
Na fara 1984 yau shekara 40 kenan da fara yin rubutu, kuma na fara yin rubutu da gajerun labarai da nake aikawa kasar Jamus. Akwai wani shiri da suke yi Taba ka Lashe, 1985, 1986 1987, a wannan lokacin na yi labarai da yawa ana biyana kudi Duertch Mark 100 zuwa 150 ya danganta da tsawon labarinka minti 1 zuwa 15 ake karanta labarina. To a wannan lokacin na fara, amma ban buga littafi ya fita kasuwa ba sai a 1990 watau yanzu shekara 34 kenan da fara buga littafina mai suna Inda So da Kauna.
Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta?
Za su kai guda 25 wadanda na buga su kuma sun fita kasuwa kuma sun shiga hannun al’umma.
Har yanzu kana bugawa ko kuma ka daina?
Har gobe, har jibi In sha Allahu in dai ina raye, ba ni da wani aiki da ya wuce buga littatafai watau Publishing da printing da kuma abin da ya shafi dab’i da kuma sayar da littattafai na a makarantu tun daga jami’o’i da kwalejin ilimi da sakandare duka. Bana littafina na cikin wadanda za a karanta a manyan makarantun sakandare na Arewacin Nijeriya duk inda ake koyar da Hausa, to za a karanta Malam Zalimu a matsayin wasan kwaikwayo kuma za a shekara uku ana karanta shi a sakandare babba daya biyu uku. Sannan bayan shekara uku kuma za a karanta a WAEC da NECO da JAMB kenan za a yi kimanin shekara biyar ana karantawa a makarantun babbar sakandare na Nijeriya.
Me ya ba ka sha’awa ka fara yi rubutu, sannan kuma na san dai rubutu bai wa ne ba za a ce wai an koya maka ba amma ka san a kowanne lamarin rayuwa akwai ubangida, shin ka kwaikwayi wani ne ko kuwa salon rubutunka ne na kanka ko wani ne ya dora akan harkar rubutun?
To ni tuntuni ina da basirar bayar da labari, akwai yayata da ake kira Binta, muna zama mu yi wasan kwaikwayo da ita. A kunna tif rikoda mu dauki murya, na yi muryar mace na yi ta namiji na yi ta tsoho da ta yaro a wannan lokacin sai mu kunna muna saurare. Don haka ina da basirar bayar da labari, saboda haka a 1984 sai na fara rubuta gajerun labarai. Gaskiya ba wai wani na kwaikwaya ba, idan kana da baiwar rubutu to kana da ita, kuma shi labari kana iya samunsa daga cikin al’ummar da kake zaune na abin da yake faruwa. Abin da ka gani da abin da ya faru da kai da kuma wadanda ya faru ga ‘yan uwa da abokan arziki. Ni dai ban yi irin zafin karance-karancen nan ba da ake yawan yi. Akwai wani littafi da na san na karanta mai suna Nagari Na kowa wanda nake jin Jabiru Abdullahi ne ya rubuta. Wannan ne littafina na farko da na soma karantawa. Don haka idan na ce ba kallon wasu na yi na soma ba, illa dai ina bayar da labari da ma, sai aka ba ni shawarar cewa ya kamata labaran nan na mayar da su littafi.
Da yawa ana samun matsaloli a farkon fara rubutu. A naka bangaren wadanne matsaloli ne ka taba fuskanta a farkon rubutunka. Yawanci marubuta na gamuwa da wani cikas da ake kira ‘Kan Ta Kile’. Shin ka taba fuskantar hakan?
Ni ban samu wannan matsalar ba, saboda na farko da na fara gajerun labarai da ma ana biyana, da na zo zan buga littafi mai suna Inda So da Kauna (1990) na yi ta fafutukar yadda zan yi. Lokacin Naira dubu biyar nake nema kawai amma ba ni da ita. Shi ne kudin da za a buga guda dubu daya. To akwai wani maigidana ana ce masa Alhaji Nura na Alhaji Sharif Bala Gabari, shi yana buga littatafai da kansa na Arabiyya kuma makwabcinmu ne a nan Sani Mai Nagge ga gidanmu ga nasa. Da na nuna masa littafin nawa sai ya ba ni shawara yadda za a yi typesetting. Lokacin ma babu kwamfutoci da ake yin rubutu a yanzu. Rubutun inji ne ake zuwa a wanke dodon a yi fileti. Haka aka yi aikin aka sayi takarda aka yi aikin. An kashe Naira dubu biyar aka sayar da shi Naira dubu takwas. Saboda haka ni babu wanda ya yi min kan ta waye ko wani abu makamancin haka. Shi yana bugawa, ni kuma na san manyan marubuta ina zuwa wajensu, wadanda suka hada da malaman jami’a kamar su Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, Allah ya jikansa. Su Farfesa MKM Galadanchi Allah ya jikansa. Su Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da sauran malamai wadanda duk na hadu da su a wannan lokaci. Sun sanni na sansu kuma na kan je gidajensu da sauran abokaina marubuta irin su Yusuf Adamu, su Nasiru Mudi Giginyu, su Lawan Adamu Giginyu duk mun saba da su kuma muna hulda da su.
Kana cikin wata kungiya ce ta marubuta ko kuwa dai kadai kake ayyukanka?
A farko ba ni da kungiya. Daga bisani na hadu da Dan Azumi Baba da Balaraba Ramat Yakubu da Aminu Hassan Yakasai da Badamasi Shuaibu Burji da Alhaji Hamisu Makwarari da Aminu Abdu Na’inna, sai muka kafa kungiya, muka rada mata suna Raina Kama Ka ga Gayya. Wannan ce kungiyarmu farko da muka yi ta yi har kuma aka zo aka batun ANA da sauransu.
A cikin rubutunka wanne ka fi so, kuma wanne ne bakandamiyarka?
Ni a wajena littafin Wani Hanin Ga Allah shi ne bakandamiyata saboda ya tabo batun siyasa, batun karatun jami’a batun matsalar zama karkashin mahaifin wani ba naka ba da dai sauran abubuwa makamantan haka. Ko yanzu na zauna na kalle shi nakan ji dadi da murnar cewa rubutuna ne wannan. Kuma abubuwan da na fada shekaru 20 har yau suna faruwa kuma a cikinsu wasu ma muke a halin yanzu, amma mutane sun fi son Inda So da Kauna shi ne bakandamiyarsu. Kuma ko a wajen saidawa na fi sayar da Inda So da Kauna, na sayar da sama da kwafi dubu 300 a iyakacin lissafina.
Ga ka marubuci, kuma yanzu kwatsam sai aka tsince ka a duniyar finafinai. Ta yaya aka yi ka soma shiga fim?
Lokaci daya da wasan kwaikwayo da rubutu duk tare na fara. A 1984 bayan na shiga Masallaci Adult Ebening Class watau makarantar ilimin manya ta Masallaci a Shahuci, sai na ci karo da wata kungiya ana ce mata Gyaranya Drama wadda Alhaji Mudi Gyaranya yake shugabanta, sai muka ci gaba da hulda da su a matsayina na mamba dinsu. To ta nan na fara wasan kwaikwayo na dandali, har tafiya ta yi tafiya aka zo aka shiga harkar shirya finafinai inda na fara shirya fim dina mai suna Inda So da Kauna a 1994 ya fito a 1996 zuwa 1997. Don haka da rubutu da wasan kwaikwayo tare na fara su amma fa na dandali shekara 40 baya.
Ya zuwa yanzu ka yi finafinai da yawa ne?
Eh kamfanina ya yi fim kamar 18 zuwa 20 wanda na kamfanina ne. Kai tsaye nawa ne, ko kuma wani ne ya zo ya rabu da ni, aka yi amfani da sunan kamfanina aka shirya. Sannan kuma na fito a cikin fim din Inda So da Kauna a matsayina na jarumi a wannan shekara ta 1994, wanda yanzu shekara 30 kenan. Bayan haka kuma, a duk fina-finan kamfanina na kan fito sau daya sau biyu watau Cameo Appearance ba na fita da yawa, sai dai na bayar da umarni ko na rubutu. Daga baya kuma bayan ma na tafi hutun harkar wasan kwaikwayon da ma fim din sama da shekaru 10 sai wani dalili ya sa aka dawo da ni cikin fim a matsayin jarumi. A wani fim da za mu yi da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu wadda ita ce ta dauki nauyin fim din kuma tana daya daga cikin masu shiryawa ni da ita. Ana kiran fim din Juyin Sarauta. Dalilin shiga cikin fim din kuma shi ne, ina daya daga masu shirya shi, akwai Sarki da zai fito, sai ya kasa. Ni da farko matsayin sallama aka ba ni, da ya kasa, sai Hajiya ta matsa mini na karbi matsayin Sarkin. Daga nan kuma na yi fim din Bilkisu, shi ma wani fim ne mai dogon zango na marigayi Umar Sa’id Tudunwada, Allah ya jikansa da gafara. An yi shi ne Rukuni biyu babi 26 amma fito kasuwa ba. Sai kuma fim din Kwana Casa’in shi ma da ya zo aka tsince ni a ciki.
Ka taba zuwa kasashen waje ne sannan a gida Nijeriya kamar jihohi nawa ka ziyarta?
Na je kasashen duniya kimanin 20. A kasashen Turai na je Italiya da Faransa da Ingila da Jamus da Holand. A Afrika kuma na je kasashe 15. A gida Nijeriya kuma na zagaya kusan duka jihohin nan 36, illa dai inda ban shiga bai wuce jiha daya ko biyu ba. Watau Bayelsa da Jihar Ribas.
Kana da wata kalma da za ka fada wadda ba mu tattauna ba kamar a ce shawara ko tsokaci ko ma dai mene ne akan harkar rubutu ko fim.
Shawarar da zan yi ga sababbin marubuta ko sababbin masu son su shiga harkar fim. Duk wanda zai yi rubutu ya kula da addininsa da al’adarsa. Domin adabi madubin rayuwar al’umma ne kuma idan ka yi rubutu yanzu ya zama ba naka ba, ya shiga duniya wani idan ya gani a Ingila ko a Faransa ko a Jamus, idan ka ba da wata dabi’a ko al’ada wadda ba irin ta Bahaushe ba, shi zai kalli Bahaushe ne matukar labarin Bahaushe kake bayarwa, zai dauke shi a haka. Idan kuma a fim ne ka shiga, shi ma ya kamata ka kula da addini da al’ada wajen wakiltarsu a harkokinka. Wata rana muna taron UNESCO a Bamako kasar Mali, wani Dakta Haidar a cikin marubuta sai ya ce ya ga mutanenmu a cikin lambu ana rawa ana waka. Ko da ma haka Hausawa suke? Na ce, a’a, ba haka al’adun Hausawa suke ba, wannan tasirin bakin al’adu ga rayuwar Bahaushe da kallon fim din Indiya da sauransu, amma Bahaushe yana da rawarsa ta gargajiya, akwai inda mata ke rawa irin tasu, akwai rawa iri daban-daban da kabilar Hausawa ke yi da sauransu. Don haka, na ce masa ba haka ba ne. To kin ga wannan wakilci ne da ake yi mana baibai wanda ba daidai ne da al’adar tamu ba. Kuma ina kira ga sababbin masu son shiga da su kula da wannan da kuma su masu shiryawa da masu bayar da umarni, ba a ce kada a yi nishadi ko sauran abubuwa ba tun da fim akwai ilmantarwa, fadakarwa da nishadantarwa, to idan za a yi sai a dinga kula da wakilcin al’adarmu. Wannan ita ce shawarar da nake son na ba wa dukkan masu son shiga wannan harka.
Akwai mantuwar da na yi. Na so na yi wannan tambayar tun farko. Yanzu karance-karance ya yi karanci, kana ganin me ya jawo haka?
Tasirin wayar hannu da intanet da dandalin sada zumunci da ake kira social media groups. Don kin ga yanzu akwai ‘Online Writers’, wadanda a yanzu mata ne ke da rinjaye a marubuta da ‘yan kadan daga cikin mazan suna nan a kungiyoyi daban-daban kuma suna bayar da labarai sadaka, kyauta ana ta karantawa babu ko kwabo, ‘yan kadan ne daga cikinsu da suka samu dama da karbuwa suke dan sa kudi ana sa musu kudi ko kati ana dan aika musu abin da suke samun sayen Data da sauransu. Suna nan a WhatsApp, Watpad da sauransu. Saboda haka za ki ga babu cinikin da ake yi sosai in dai ba a ce littafinka ya shiga manhajar makarantar jami’a, ko ta kwaleji ko kuma ta sakandare ko wani waje dai da ake karantawa. Ko kuma aka samu aka saya domin dalibai a ajiye musu. Amma in domin ka buga ne ka kai kasuwa domin nishadi ba a ciniki sosai a gaskiya.
Kana ganin kenan yanzu kasuwar littafi ta mutu kenan ko kuwa akwai yiwuwar dawowa
A’a ba za a ce ta mutu ba, sai dai a ce ta yi karanci ko kuma ta yi kasa. Domin kamar yadda na ce, ai ana sayen littafi domin dalibai, kuma mu da muke rubutun wasan kwaikwayo ai ga shi yanzu ina gaya miki, an sa shi a manhaja za a shekara biyar ana karanta shi. Kuma muna sa rai a cikin wannan shekara biyar din za a saya da yawa. Sai dai kamar yadda kika sani Social Media din ta zama abin da ta zama, da yawa za ki ji suna cewa, akwai shi online? Ni kuma ban taba saka ko daya a cikin littafaina online ba. Saboda kawai na saba wannan nake yi, mai yiwuwa nan gaba zan yi. Amma dai gaskiya a yanzu babu cinikin littafi kamar da in dai ba wanda aka saka domin a nema a karanta a makarantu ba.
Tsakanin harkar rubutu da harkar fim wanne ka fi so?
Na fi son rubutu. Saboda ya yi min riga da wando. Da shi na yi suna kafin a sanni a fim. Domin wancan da na yi a baya, Inda So da Kauna an sanni amma kuma na tafi hutu na kyale, sai daga na dawo. Ba domin haka ba duk wadanda suka sanni da harkar rubutu suka sanni. Duk wadanda suka sanni a jami’oi na duniya ba a fim suka sanni ba, a rubutu suka sanni. Duk jami’o’i da ake yin harsunan Afirka a duniya wadda na sani da wadda ban sani ba za ki ji da sunana a rubuce a can. Ko yanzu mutum ya je Google ya rubuta Ado Ahmad Gidan Dabino zai ga inda aka yi bayani kaina da littafaina da jami’o’i da laburaren da ake da su. To kin ga a rubutu aka fi sani na. A yanzu ne dai da nake harkar fim wasu ke sani na. A baya da na yi Inda So da Kauna wadanda za a ce sun san ni ba yara ba ne domin duk wanda yake shekara 25 yanzu ba zai ce ya san Inda So da Kauna ba sai dai iyayensa ko yayyensa su ba shi labarinsa. To kin ga na fi son rubutu, saboda shi nake yi, da shi nake bugawa nake saidawa tun da ba rubutawa kawai ba, ina Publishing, watau wallafa wa jama’a nasu ayyukan. Kuma kamfanina ya buga littatafai sama da 300 daban-daban a tsawon shekarun nan. Har daga China an kawo min aiki, daga Nijar da sauran kasashe. Kuma duk tafiye-tafiyen nan da na ce na je kasashe 20 ba fim ne ya kai ni ba, littafi ne ya kai ni.
Wanne abu ne ba za ka taba mantawa da shi ba da ya sa ka farin ciki da kuma wanda ba za ka manta da shi na bakin ciki a harkokinka na yau da kullum.
Abin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne, lokacin da aka ce sunana ya fito a jerin wadanda gwamnatin Nijeriya za ta karrama da lambar yabo ta kasa watau M.O.N, domin ban yi zato ba, ban yi tsammani ba wani ya kirawo ni ya ce na bayar da sunana da CB dina. Daga haka sai da aka shekara biyu, na ma manta da zancen. Wata rana muna taro a Jami’ar Bayero ta Kano sai wani ya ce min ya ga sunana a cikin jerin wadanda za a karrama da lambar yabo ta kasa. Nan da nan na ce, ba ni ba ne. Kuma wallahi da gaske nake na dauka ba ni din ba ne. Ya ce, a’a duba dai. Muna dubawa a Premium Times sai ga sunana. To wannan kam ba zan manta shi ba. Daga nan na tafi Abuja ni da matata da babbar ‘yata Fatima. Shugaban kasa ya makala min wannan lambar ta M.O.N. A cikin marubuta sa’o’ina da suka fara rubutu a 1990 zuwa yau ni kadai na samu wannan lambar. Tun bayan Abubakar Imam a sanina, ban san wani marubuci na hikaya da ya samu irin wannnan lambar yabo ba. To kin ga wannan abin jin dadi ne, tamkar mun bude kofa ne, kuma fatan a ce wasu ma sun biyo baya. A ce wanda yake bai yi zurfin karatu ba, daga makarantar dare ya yi kaza da kaza ya samu babbar karramawa akan harkar da yake yi. Abu ne na farin ciki, abu ne na jin dadi ga dukkan marubuta tun da na zama tamkar zakaran gwajin dafi gare su. Su ma a yanzu suna iya yin tinkaho na cewa a cikinsu an samu wanda ya taba samun lambar yabo ta kasa. Kodayake a fim akwai wadanda suka samu irin wannan lambar yabo da dama. Wannan shi ne abin da ba zan taba mantawa da shi ba kuma har kullum ina tunawa da shi.
Sannan abin ba zan manta da shi ba shi ne lokacin da nake shugabancin marubuta na Nijeriya reshen Jihar Kano watau ANA, mun yi rigingimu da hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano watau Censorship Board wadda Abubakar Rabo ke shugabanta. Na samu kalubale da yawa, saboda ana nema na a kama ni. Saboda na ce marubuta ba za su yi kaza da kaza ba, wanda muke ganin ba daidai ba ne a ce za mu yi rijista ta daidaiku ba. Wannan rigimar ba zan manta da ita ba saboda ban taba shiga irin ta ba. Sannan kuma, wadanda na yi ta fadan domin su watau marubuta da aka gama fadan suka zo suka ci dunduniyata, suka yi ta yi mini abu na rashin jin dadi wanda ni a tunanina wanda ya tsaya ya yi muku fafutuka ya kare muku kima da mutunci da darajarku, to bai kamata wasu daga cikinku su zama munafukai ba, ita waccan hukumar ta rika amfani da ku a ce za a yaki wannan mutumin da ya yi muku kokari ba. Kuma suka yi ta yin dadin bakin cewa za su bayar da kudi, ko za su yi abu kaza da kaza. Kuma kun yi rashin kirkin, ina shugabancin aka ce sai na sauka aka kafa kwamitin rikon kwarya. Na sauka kuma ita hukumar da ta kira su ta yi musu wannan abin, saboda na dame su. Na zame musu karfen kafa, saboda haka sai suka ce idan kuna son gwamnati ta yi muku abu kaza da kaza sai kun cire wannan shugaban naku. Suka zo suka cire ni. Na sauka bayan na yi shekara uku. Suka je suka yi abinsu, kuma abin da ta ce za ta yi musu din ba ta yi ba, ta yaudare su. Daga bisani wasu suka gane cewa abin da suka yi ba daidai ba ne, wasu suka gane cewa kuskurensu wasu kuma ba su gane ba. Kuma muna nan tare da su, kuma dai kullum gani suke yi ina gaba da su. Ko suna so ko ba sa so, ba yi na ba ne, yin Allah ne. To wannan abin da rayuwata ta harkar rubutu ba zan manta da su ba, mai dadi da mara dadi, ka yi ta fada akan mutane. Daga baya su kuma su zo su yake ka ko su ci mutuncinka ko su yi maka wulakanci. To wannan shi ne abin da ba zan manta da shi ba.
Wane kalar abinci ka fi so?
Tuwo kowanne iri, na dawa ko na masara ko shinkafa in dai tuwo ne da miyar yauki, kuka ko kubewa da man shanu da yaji.
Wanne irin launi ka fi so?
Ni ba ni da wani zabi kowanne irin launi amma na fi son shaddoji a cikin tufafi.
Yanayin gari fa?
Na fi son yanayin zafi ba na son sanyi
Me ya sa?
Sanyi na hana ni sakewa, don haka duk sa’adda na fita kasashe masu sanyin nan wando uku riga hudu nake bunjumawa, saboda bala’in sanyin can. Ana sanyi kankara na zuba, kana magana bakinka na fitar da hayaki. To gaskiya wannan lokacin ban sake ba, kuma ban taba tafiya lokacin zafi ba, duk lokacin da nake tafiya lokacin sanyi ne.
Wacce kasa kake son ziyarta nan gaba?
Saudi Arabiyya nake son zuwa. Ban taba zuwa Makka ba. Allah bai kira ni ba har yau (dariya) Ban taba zuwa ba, ita ce kullum nake ta addu’a nake gaya wa mutane idan sun je Makka su yi min addu’a kan Allah ya kira ni idan Allah ya nufa ina da rabo, amma idan ba ka da rabo babu yadda za a yi sai ka ga wani ya biya wa mutane Makka sun je, kai muma ba ka taba zuwa ba.
Me kake so a yi maka kyautarsa?
Ina son kyautar turare ina son sutura.
Masha Allahu. Wanne fata ne gare ka ga LEADERSHIP Hausa?
Ina yi mata fatan alheri, kuma lallai shi wanda ya kafa jaridar ya yi kokari. Sam Nda na san ya rasu kuma na san ya ba wa adabi gudunmawa sosai wajen bude filaye da ake hira da marubuta da sharhi da sauransu. To ina mata fatan alheri yadda ta taso tana ci gaba, Allah ya sa ta dore amin.