Karfin batiran ababen hawa masu amfani da sabon makamashi da kasar Sin ke samarwa, ya samu ci gaba a shekarar 2022, yayin da kasuwar motocin masu amfani da batir ke samun tagomashi a kasar.
A cewar kawancen kungiyoyin masu samar da batiran ababen hawa na kasar Sin, bayanai sun nuna cewa, jimilar karfin batiran da ake sanyawa irin wadannan motoci masu amfani da sabon makamashi, ya kai gigawatt sa’o’i 294.6, wanda ya karu zuwa kaso 90.7 a kan na shekarar 2021.
Kimanin batira samfuran Lithium-ion masu karfin gigawatt sa’o’i 183.8 aka sanyawa motoci masu amfani da sabon makamashin a shekarar 2022, adadin da ya karu zuwa kaso 130.2 daga na shekarar da ta gabata, haka kuma ta mamaye kaso 62.4 na jimilar adadin.
A watan Disamban shekarar 2022 kadai, karfin wadannan batira ya karu da kaso 37.9 zuwa gigawatt sa’o’i 36.1.
Haka kuma, a shekarar 2022, kasar Sin ta sayar da kimanin motoci masu amfani da sabon makamashi miliyan 6.89, wanda ya tashi zuwa kaso 93.4 a kan na shekarar 2021. Samar da irin wadannan motoci ma ya karu da kaso 96.9 a kan na shekara daya da ta gabata, zuwa motoci miliyan 7.06, kamar yadda bayanai daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin suka bayyana.
A cewar kungiyar, cinikin nau’in irin wadannan motoci ya karu a shekarar 2022 zuwa kaso 2.1, inda aka sayar da motoci miliyan 26.86 a kasuwar motocin mafi girma a duniya. (Fa’iza Mustapha)