ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karramawar Shugaban Kasa Ta Kara Min Ƙaimi – Sadiya Farouq

by Sulaiman
3 years ago
Sadiya Farouq

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq
ta bayyana jin daɗin ta bisa karramawar da ta samu ta NEAPS, inda ta ce abin zai ƙara mata ƙaimi da jajircewa a aiki.

Minista Sadiya ta ce: “Wannan wani muhimmin zango ne, musamman a rayuwa ta, domin wannan karramawa shaida ce ƙarara ta gamsuwar da aka yi da ‘yan nasarorin da na samu a wajen ayyukan da na yi wa jama’a ya zuwa yanzu da kuma alhakin da aka ɗora mani a fagen ayyukan inganta rayuwa da jinƙai a cikin ‘yan shekarun nan.

  • Ambaliyar Ruwa: Ku Kwashe Jama’ar Da Suke Zaune A Yankunan Magudanun Ruwa — Sadiya Farouq

Daga nan sai ta bayyana cewa “ina so in ƙara miƙa matuƙar godiya ga mai girma Shugaban Ƙasa saboda damar da ya ba ni na yi wa ƙasa ta aiki a matsayin Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, sannan ta hanyar wannan muƙamin na yi ƙoƙarin bautata wa ɗimbin mutane marasa galihu waɗanda ke cikin buƙatar a inganta rayuwar su da taimakon jinƙai cikin gaggawa a faɗin ƙasar nan.

ADVERTISEMENT

“Haka kuma ina godiya matuƙar gaske ga kamfanin ‘TBS Media’ da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da su ka ga dacewa ta har su ka ba ni wannan babbar kyauta ta NEAPS ta shekarar 2022 a ɓangaren ayyukan jinƙai, kuma su ka ɗora ni kan matakin shiga da’irar sauran manyan ‘yan Nijeriya waɗanda su ma aka karrama su tare da ni a yau.”

Ministar ta sha alwashin za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarin ta wajen yi wa ƙasar nan aiki wanda yin shi ne gudunmawar ta wajen taimakawa a tsamo Nijeriya daga cikin matsalolin da su ka addabe ta.

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Mai taimaka wa ministar a fagen aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta yi ƙarin bayanin cewa wannan kyautar karramawa da aka yi saboda aiki ga jama’ar Nijeriya “manufar ta ita ce a karrama muhimman ayyukan da aka yi wa jama’a a Nijeriya ta hanyar gudunmawar da jama’a ɗaiɗaiku da jihohi da mutanen unguwa su ka bayar wajen shugabanci da aikin jama’a da jinƙai.”

In dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranci miƙa waɗannan kyaututtuka ga Minista Sadiyya da wasu mutum 44.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace
Rahotonni

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025
Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda
Rahotonni

Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

December 19, 2025
Next Post
NDLEA Ta Kama Wasu ’Yan Kwaya 4 Da Ake Nema Ruwa A Jallo Kan Mu’amala Da Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Kama Wasu ’Yan Kwaya 4 Da Ake Nema Ruwa A Jallo Kan Mu’amala Da Miyagun Kwayoyi

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.