A kwanan baya ne, Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC) ta bayyana cewa, an samu rahoton karin yawan kananan yaran da aka yi watsi da su, wadanda suka kai sama da 1,300, tare da kuma take wasu ka’idoji.
Ofishin Sakataren Hukumar ne, ya bayyana shi wannan rahoton a watan Oktoba na shekarar data gabata, inda rahoton ya nuna matukar damuwarsa kan karin yawan adadin yaran a cikin kowane wata daya.
- Takardun Kuɗi Sun Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 4.8 Duk Da Ƙarancin Kuɗi A Nijeriya
- Me Ya Sa Fursunoni Masu Jiran Hukuncin Kisa Ke Ƙara Cunkoso A Gidajen Yarin Nijeriya?
A kan wannan lamarin ne, wasu kwararru suka yi gargadin cewa, yin watsi da yaran, na kara yin kamari, inda kuma irin wadannan yaran ne, za su iya cin karo da fuskantar cin zarafin su, take hakkinsu da dai sauran wasu abubuwa.
Kazalika, rahoton Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato (UNICEF), mai taken, “Matsayin Yara A Duniya A 2024” ya bayyana cewa, rayuwar yara ta nan gaba lalle tana a cikin hali na rashin tabbas.
Bugu da kari kuma, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, a sakonsa na bikin ranar yara ta duniya, ya bayyana kaduwarsa kan cewar, a wannan karnin na 21, abin takaici ne, ace, yara na zama a cikin yunwa, rashin samun ilimin zamani da kuma gazawar samar masu da kayan duba lafiyarsu.
António ya ci gaba da cewa, abin kunya ne a ce, alummomin sun bar yara a cikin talauci da fadawa a cikin annoba.
Ya kara da cewa, makomar Nijeriya a yanzu da kuma ta nan gaba, ta dogara ne gabadaya a kan kulawa da rayuwar yara, inda ya sanar da cewa, babu wata tantama da ake yi yara da matasa, sune manyan gobe, musamman ayi la’akari da cewa, sune suka fi yawa a cikin al’umma.
Sai dai kash! ana ci gaba da kalubalantar makomar Nijeriya, duba da yadda yara a kasar, suke ci gaba da fuskantar kalubale iri-iri na rayuwa, ciki har da yadda suke ci gaba da fuskantar talauci, fadawa a cikin rikice-rikice, rashin samun ilimin boko da kuma rashin samun kayan da za a duba lafiyarsu.
Wannan babban abin bakin ciki ne, ganin cewa, kashi 47 na yaran kasar sun kasance ‘ya’yan talakawa ne inda kuma kashi 67, ke a cikin nau’uin talauci
An kiyasta cewa, a watan Satumba na 2024, adadin yara masu shekaru daga shida zuwa goma sha hudu ne, wato miliyan 18.3, ba su zuwa makaranta.
Wannan adadin ya hada da, yara miliyan 10.2 da suka kamata ace suna zuwa makarantar Firamare ko ta Sakandare da suka kai adadin miliyan 8.1.
Kungiyar da ke kare ‘yancin yara a 2024, ta kiyast cewar yaran sun kai sama da yara ‘yan Nijeriya miliyan daya, na fuskantar rashin abinci mai gida jiki cikinsu har da yara miliyan 1.8, da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin samun abinci mai gina jiki.
Sai dai kuma, ana ganin cewa, wasu iyayen na yin watsi da ‘ya’yansu ne,saboda kalubale na matsin tattalin arziki da wasu ‘yan Nijeriya, ke ci gaba da fuskanta tare da kuma rashin samun wadataccen abinci.
Wannan matsalar ce, ta sanya wasu iyayen suka rungumi tsarin kayyade samun, musamman ma domin su samu damar ci gaba da daukar nauyin sauran ‘ya’yansu, da suka haifa
Asusun na UNICEF, ya bayyana cewa, nan da shekara ta 2050, a duk haihuwar daya a cikin haihuwa sha uku, da ta aka samu a Nijeriya, hakan na kara yawan adadin alummar kasar, wanda hakan ne kuma ke nuna karin wata bukatar, kara kulawa da yaran.
A saboda haka ne, ya kamata a gyara tsarin kayyade samun ciki, ba kawai shi tsarin ya kasance a matsayin wata magana ba, amma ko don saboda matsayin kulawa da lafiya da kuma kara bunkasa kasa.
Bugu da kari kuma, hakan zai iya taimakawa wajen samu daukar juna biyun da ba a shirya masa ba, da kuma magance sauran matsalolin kashe kudade.
Nijeriya za ta iya rage yawan yara miliyan 10.5, da suka daina zuwa makaranta zuwa kashi 90, idan har masu fada aji a kasar, sun rungumi tsarin samar da ilimin boko kyauta da kuma samar da damar samun duba lafiya kyauta.
Lokaci ya yi, da Nijeriya za ta dai na yin korafi a kan yawan adadin yaran da ba su zuwa makaranta, amma ta mayar da hankali, wajen lalubo da mafita, domina tabbatar da magance matsalar.
UNICEF ta bayar da shawarar cewa, ya kamata a zuba hannun jari a fannin ilimin zamani, musamman ma domin amfanin yaran.
A saboda haka ne, muke bada shawar vangarorin hukumomin tsaro da na shari’a na kasar, da su tabbatar da cewa, ana hukunta masu cin zarafin yara.
Dokar kare hakkin yara (CRA), wadda ta zamo doka a 2003, ta tabbatar da ‘yancin, yara da shekarun su suka fara daga 18.
Hakanana ma, dokar ta kuma yi bayani a kan batutuwa masu dama, da suka hada da samar da kulawa da lafiyar yara, haramta yin auren wuri ga su ‘ya’ya mata da kuma gundunmawar da gwamnti za ta bayar ta kare ‘yancin yara.
Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yancin yara, ana kallon wannan yarjejeniyar, a mtsayin mafi girma a cikin tarihi.
Kazalika ma, yarjejeniyar, ta tabbatar da ci gaba da dorewar rayuwar yara, bunkasa rayuwarsu, ba su kariya da kuma shiga a dama da su kan abuwan da suka shafi ci gabansu.
Sai dai, abin takaicin shi ne, a namu ra’ayin, rashin wanzar da irin wadannan ‘yancin na yaran, hakan ne ya sanya ake sa yaran yin aikin wahala, sace su da kuma yin watsi da su.
A nan, muna kiran gaggawa da gwamnati ta kara kaimi wajen kara jaddada dokar bai wa yaran kariya da kuma magance taskun da suke ci gaba da fuskanta na matsin rayuwa, da suke ci gaba da fuskanta.
Wannan jaridar bisa la’akarin da ta yi a 2024, jihohin kasar nan 24 ne kacal, daga cikin jihohi 36 na kasar ne suka rungumi tsarin dokar bai wa yara kariya.
Sauran jihohin da ba su rungumi wannan dokar ba sun hada da; Gombe da kuma Bauchi.
Mun damu matuka, kan yadda ake kara samun yawan yaran da ba a kulawa da rayuwarsu a kasar.
Babbar Darakta ta Asusun UNICEF Catherine Russel, ta yi ikirarin cewa, hukuncin da shugabannin duniya suka yanke a yau ko kuma suka gaza dauka, zai fayyace wacce irin rayuwa ce, yara a duniya, za su iya tsintar kansu a ciki.