Bayan zaman lafiya da aka samu a ‘yan shekarun nan a yankin kudancin Jihar Kaduna, al’amurra sun kara runcabewa a inda aka samu karuwar kashe-kashe mutane da asarar dukiyoyi na rashin kan gado.
A ranar Lahadin makon jiya ce ‘yan bindga suka kai wani wawan hari inda suka hallaka mutum 28 a wasu hare-hare da suka kai a kauyukan Malagum 1 da Sokwong da ke masarautar Kagoro a karamar hukumar a Jihar Kaduna.
Wannan harin ya auku ne bayan akalla kwanaki 5 bayan harin da aka kai kauyen Malagum 1 in da suka kashe mutum 3.
Kamar dai yadda aka saba, al’umma da kungiyoyi da dama sun yi Allah wadai da hare-haren, wanda yana daga cikin abubuwan da ke tayar da hankalin mazauna yankin saboda har yanzu gwamnati bata gano bakin zaren ba.
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna ta yi tir da harin, tana mai cewa, harin da aka kai yankin na kudancin Kaduna abin takaici ne da ya kamata al’ummar Nijeriya su yi tir da shi.
Haka kuma gwamnatin Jihar Kaduna, Kungiyar Kiristocin Nijerriya ta Jihar Kaduna da jam’iyyar LP,haka kuma mataikmakin dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar AAC, Barsista Haruna Magashi ya sanar da cewa, in har jam’iyyar su ta samu nasaarar darewa karagar mulkin kasar nan a shekarar 2023 za ta tabbatar da samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin na kudancin Kaduna, jam’iyyar ta kuma ce, yawaitar hare-haren abin takaici ne ya kuma kamata a hada hannu don kawo karshen lamarin gaba daya.
A sanarwa da ta fitar, gwamnatin Jihar Kaduna, ta hannun kwamishina tsaron cikin gida, Aruwan Samuel, ta mika ta’aziyyarta ga iyalai da ‘yanuwan wadanda suka rasa rayuwa da dukiyoyinsu.
Gwamna Nasir El Rufai, ya yi tir da harin yana mai cewa, tsabagen rashin imani ne musamman ganin yadda gwamanti ke kokarin tabbatar da samar da zaman lafiya a sassan jihar ta hanyar samarwa da jami’an tsaro dukkan kayan aikin da suke bukata, da kuma kakarin da gwamnatin ke yi na jawo masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya ashin samar da tsaro a cikin makon da ya gabata.
A nata bangaren, kungiyar CAN reshen Jihar Kaduna ta ce, har zuwa yanzu ba a kai ga kamawa tare da hukunta wadanda suke kashe mutane a yankin kudancin Kaduna ba, ta haka ne kawai za a iya samun tabbacin kawo karshen ayyuykan ‘yan ta’addan gaba daya.
Ita kuwa kungiyar Al’umma yankin Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta bayyana cewa, a watan Afrilu na wannan shekarar in kawai an kai hare-hare ga al’umma fiye da 148 a ciki shekara 6 a yankin na kudancin Kaduna yayin da kuma aka tarwatsa mutane fiye da 200,000 daga gidajensu.
Da yake bayani a kan yadda ayyukan ‘yan ta’addan ya shafi al’ummar yankin a cikin shekara 6, shugaban kungiyar SOKAPU, Hon. Jonathan Asake, ya bayyana cewa, harkoki ‘yan ta’addan ya kai ga kora fiye da mutum 200, 000 da ke zaune a garuruwa 148 na yakin kudancin Kaduna a halin yanzu suna zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira.
Tabbas bai kamata a zura ido a na kasha-kashen mutane tare zubar jini ba na ba gaira babu dalili a yankin kudancin Kaduna, dole Gwamnati ta tabbatar da kawo karshen wannan mummuna aiki ba tare da bata lokaci ba, ba kawai yankin Kudancin Kaduna ba har da sauran sassan Jihar Kaduna dama Nijeriya gaba daya.
Babu tantama ayyuka sun yi wa sojoji da jami’an tsaronmu yawa a inda suke kokarin samar da zaman lafiya a sassan Nijeriya. A yayin da ake cigaba da yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ‘yan ta’addan na cigaba da tagaiyara al’umma a yankin Arewa ta Yamma da Arewa ta Tsakiya. Tabbas a ‘yan kwanakin nan jami’an tsraro na samun nasarar da ya kamata a kan ‘yan ta’addan amma a har yanzu ‘yan ta’addan na cigaba da harkokinsu na garkuwa da mutane da sauran manyan laiffuka a sassan Nijeriya wanda hakan yana matukar sanya damuwa ga al’umma gaba daya.
A kididdigar da ta fitar a shekarar 2019, Hukumar sanya ido a kan ayyukan ‘yan ta’adda (Global Terrorism Inded (GTI) ta nuna cewa, Nijeriya ce a kan gaba a cikin kasashen da ‘yan ta’adda suke cikin karen su babu babbaka, kasashen Irak da Afghanistan ne kawai a gaban Nijeriya.
Ra’ayinmu shi ne, yakamata gwamnatin Jihar kaduna ta tabbatar da aiwatar da rahoton kwamitin da ya binciki rikicin Zango-Kataf da aka yi a shekarun baya. A shekarar 2020 ce gwamatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin mutum 8 don ta tantance rahottanin binicke biyu da aka yi a kan yawaitar rikici a karamar hukumar Zangon-Kataf. An shirya cewa, kwamitin zai tantance ayyukan da kwamitin Maishari’a Rahila Cudjoe ta yi ne don ta samar da matakan da gwamnati za ta bi don kai wa ga karshen rikice-rikicen da ake fuskanta.
Abin takaici kuma shi ne, yanzu kusan shekara 2 kenan bayan kafa kwamitin amma babu wani labarin halin da ake ciki.
Wani karin abin takaicin kuma shi ne, gwamnati ta tabbatar da gano daya daga cikin manyan dalilan da suke aukar da riikice-rikice a yankin kamar yadda kwamitin Mai Shari’a Cudjoe ta bayyana a binciken da ta yi a kan rikicin Zangon kataf na shekarar 1992, kuma sune ke cigaba da haifar da rikice-rikicen har zuwa yanzu shekara 28 kenan da suka wuce.
Ra’ayinmu shi ne, babbar dalilin da ya cigaba da haifar da rikice-rikice a Jihar Kaduna shi ne rashin aiwatar da rahotannin kwamitocin da aka kafa a baya suka bayar musamman rashin hukunata wadanda suka yi kisan al’umma ba tare da tausayi ba.
Duk da haka, gwamnmati na bukatar goyon bayan dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada ‘yansiyasa malaman addini da sarakunan gargajiya don kawo karshen kashe-kashe a yankin kudancin Jihar Kaduna. Dole a fadakar da al’umma a kan bukatar zaman lafiya a tsakanin kabilu da addinan da ke yankin na kudanci dama sassan Jihar Kaduna gaba daya.
Haka kuma yakamata a tabbatar da an hukunta wadanda aka tabbatar suna da hannu a kasha-kashen al’umma domin hakan ya zama darasi ga masu niyyar aikata irin wannan ta’asar hakan kuma zai karfafa fahimtar juna a tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp