Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce tsakanin watan Janairu da Yulin bana, adadin mutanen da suka yi shige da fice ta tashoshin shigowa kasar Sin sun kai miliyan 341, wanda ya karu da kaso 62.34 bisa dari kan na makamancin lokacin a bara.
Tabbas ci gaban da aka samu a watannin 7, na da nasaba da managartan manufofi da matakan da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa. Misali, manufar shiga kasar ba tare da shaidar biza ba ga wasu kasashe da kyakkyawan tsare-tsaren sufuri da fadada bude kofa da ma ci gaban da take samu a dukkan fannoni, da uwa-uba tsaro da zaman lafiya, wasu abubuwa ne daga cikin dalilan da suka sanya ake samun karuwar masu ziyartar kasar.
- Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Afrika Ta Kai Wani Sabon Matsayi
- Huawei Ya Kaddamar Da Horo Game Da Tsaron Yanar Gizo Ga Jami’an Zimbabwe
Gani ya kori ji! Ta hanyar shigowa kasar Sin da ma fasahohin da zamani ya kawo mana, baki za su iya ganewa idanunsu ainihin kasar Sin da jama’arta masu kirki da kyawawan al’adunta da cimaka masu dadi, sabanin yadda kafafen watsa labarai na yammacin duniya ke gabatar da kasar Sin. Kana za su yi amfani da fasahohin zamani wajen watsa abubuwan da suka gani ga ’yan uwansu da sauran jama’ar duniya, lamarin da zai kara wayar da kan duniya game da yanayin da duniya take ciki da kuma bayyana gaskiya a zahirance.
Karya fure take ba ta ’ya’ya! Baki daga kasashen duniya daban daban na da damar ziyartar wurare daban daban na kasar Sin tare da mu’amala da Sinawa da ganin al’adun da ci gaban kasar a zahiri, lamarin da zai ba su damar gina ra’ayi ko tunanin na kashin kansu game da kasar Sin, wanda babu wanda zai iya sauyawa ko gogewa, kana za su iya fayyace gaskiya da karya don gane da karairayin da suka dade suna ji.
Har kullum kasar Sin kan ce ba ta da abun boyewa, kofarta a bude take domin jama’ar duniya su kawo ziyara don ganin wannan kyakkyawan kasa mai tafiya da zamani, dake samun ci gaba a kullum, wadda kuma ke da abubuwa masu ban sha’awa ga duk wanda ya ziyarce ta. (Fa’iza Mustapha)