Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu Mazan ke yin karyar lefe dozin ko sama da haka, alhalin ba su da halin yi.
Da yawan wasu matasan ko na ce wasu Mazan na yin karyar lefe ko da kuwa ba su da halin da za su yi yawan abin da suka yi, domin hakan na faruwa ba iya matasa kadai ba har ma da magidantan da suke da mata a gida.
- Hukumar Lafiya Ta Ankarar Da Al’ummar Jihar Neja Kan Cutar Bakon Dauro
- Ganduje Ya Gabatar Da N245.3bn A Matsayin Kasafin 2023 Ga Majalisar Dokokin KanoÂ
Duk da cewa zamani ya sauya ba kamar lokutan baya kadan da suka wuce na shekara biyar, shida zuwa goma ba.
A yanzu wasu Mazan na kara tsawwala tsadar lefe a wajen yin aure, ta yadda marasa shi suke koyi ga masu shi dan sace zuciyar dangin wadda ake so ko ita wadda ake so, ko kuma birge jama’ar unguwa da kara kankaro kai wajen jama’ar da za su ganin lefen, ko kuma abokan saurayin, ko wajen watsawa a social media.
Maza da dama na takure kansu wajen yin lefe ta hanyar bashi ko aro kayan lefen daga baya a koma a kwashe da zummar barayi sun shiga ko makamancin haka.
Sautari a yanzu wasu na yin aure da lefe me tsada masu yawa kamar dozin guda ko dozin biyu, ya yin da aka yi aure kuma sai zance ya sha bamban, ta yadda amarya za ta fara cin karo da ababen da zuciyarta ba ta taba raya mata su ba, irin wadanda idanuwanta ba su shirya cin karo da ganinsu ba, daga baya aure ya fara samun targarda.
Sai dai kuma hakan na faruwa da wasu ne ta yadda suka dorawa kansu ga duk wadda aka ta shi yi wa aure a cikin gidan dole ne ta auro wanda zai yo lefe me yawa dan fidda kunyar jama’ar gari ko dangi ‘yar su ta fita izzaka, ko kuma hakan ta rinka faruwa daga bangaren saurayin ta yadda duk wanda zai yi aure a gidan sai an yi wannan fafar sabida kankaro kima a idanuwan dangin Amarya.
Wasu kuma na yin lefe me yawa ne sakamakon sun san gidan da za su auro yarinyar ba za su taba yarda su ba da auren ‘yar su da kankanin lefe ba, dole ne ya aro rigar masu da shi ya shiga ciki daga baya komai ya sauya.
A yanzu da yawan matasa na son yin aure, wasu ma har suna da kudin hada lefen da matsuguninsu, sai dai kuma a irin karyar lefen da ake yi za a kira kudinsu da bai taka kara ya karya ba, dan ba zai kai labari ba muddin aka ce za a hada shi da kudin da ake kashewa na lefe dozin ko sama da haka a yanzu, wanda kuma shi yake kara janyo rashin yin auren matasan.
Sai dai kuma idan aka yi duba ta bangaren matan na ganin cewa yin yawan lefen na kara kima da daraja mace a gidan auren, domin kuwa zai rinka tuna irin wahalar da ya sha a lokutan da zai auro macen musamman wajen hada lefe, sabanin a bashi ita ba tare da ya sha wata wahala ba, zai rinka kallonta a wulakance, kuma ya rinka kallon mata tamkar saka riga a cire, ya yin kuwa da ya sha wahala zai sa ya rinka raga mata da wasu abubuwan, kuma ya san cewa da tsada ya samo ta ba sadaka aka bayar ba, ko da kuwa yana da shi, ya dai kashe iya ka ya dora tasa fafar da karyar dan birge al’ummar duniya na yanar gizo da danginsa dana amarya da abokan arziki baki daya. Sai dai lefe al’ada ce da aka santa tun iyaye da kakanni wadda kowa ke yi iya karfinsa, a takaice kenan.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi na Taskira ya ji ta baki wasu daga cikin Matasa game da wannan batu; Ko mene ne amfanin yin lefe dozin ko sama da haka?, Me yawan lefe ke haifarwa bayan an yi aure?, Mene ne mahimmancin yin lefe?, ko za a iya auren namijin da bai kai lefe ba?, ko kana da ra’ayin yin lefe dozin ko sana da haka?, Ga dai ra’ayoyin na su kamar haka:
Abba Fagge daga Jihar Kano Unguwar Fagge:
Abu na farko lefe mai yawa ba addini bane takure kanka ne, wannan abu ne mara kyau wanda za ka cutar da kanka. Na biyu yawan lefe idan ta hanyar karya ka yi shi bayan aure zai rushe maka aure saboda ta ga kana da shi an yi aure ta ga babu. Lefe ba shida mahimmanci sai rashinsa saboda ya janyo raguwar aure saboda tsadar rayuwa a yanzu. Idan ina da hali zan iya bawa matata duniya baki daya ba wai iya lefe mai yawa ba, amma idan babu ko da lefen ma ba zai samu ba.
Abdullahi Muhammad, daga Jihar Kano Nassarawa L.G.A Brigade Ktrs Gama “A”:
A gaskiya lefe dozin biyu ko sama da haka ga saurayi wanda yake yana da hali sosai ba laifi bane, domin zai bawa matar da zai aura damar samun sutura mai yawa. Yawan lefe abin da yake haifarwa bayan aure ga saurayin da bashi da hali shi ne; yana jawo kiyayya saboda matar za ta gane cewa yadda ta dauke ka, ba haka yake ba, daga nan raini zai shiga tsakanin su wanda daga baya zai zama silar mutuwar aurensu. Shi muhimmancin yin lefe abu ne mai kyau domin wasu matan da dama idan ba a lefen ba ba za su samu tufafi da yawa ba, kasancewar idan aka aure su wasu bai fi ayi musu kaya kala daya ba a shekara wasu ma sai su shekara biyu, ko uku ba tare da sun sami sabon kaya ba, sai kawai lefen da aka yi musu za su dinga amfani da shi. A gaskiya bani da wannan burin yi wa masoyiya ta lefe mai yawan gaske, dai-dai misali dai iya karfi na zan iya wanda ya samu. Maza masu karyar lefe a dubi Allah a daina a sani cewa fa shi Aure ba rayuwa ce ta sharholiya ba, rayuwa ce ta ibada, a dauki aure ibada ba kyalkyali ba, gina gaskiya a farkon neman aure shi ke sa bayan aure ya dore.
Amina Umar Sa’eed:
Ni a ganina ba abin da yawan lefe yake sakawa, ba wata soyayya da yake karawa, wasu kuma suna da halin yin hakan, wasu kuma ‘yan karya ne kawai. Ni ban damu da wani lefe mai yawa ba
yadda na samu na godewa allah dama albarka ake nema ba yawa ba, Shawara ta ga maza masu karyar lefe ita ce; Su daina sawa kansu karya a zukatansu saboda yin wannan karya yana jawo musu matsala, gwanda in ba su da halin yi da yawa su ba shi iya karfinsu.
Umar Sidi daga Jihar Kano:
Ni a nawa ra’ayin abin da nake gani yin lefe dozin biyu ko fiye da haka ba shi da amfani domin kuwa yawanci karya ce a ciki da neman suna, kuma an fi yin haka ne dan a birge dangin uwar Amarya ko kuma a birge kwawayen Amarya, daga karshe hakan ka iya jawo babbar matsala a zamantakewar aure, sakamakon karyar da akai wajen gina wannan auren ba a kan turbar gaskiya ba. Lefe yana da mutukar mahimmanci a Aure saboda ya samo asali ne a al’adance tun shekaru aru-aru saboda lefe shi ne; darajar ‘ya mace domin yana samarwa da mata kima a idon jama’a dama shi kansa auran nata. Shawara ga masu karyar yin lefe, karyar yin lefe na sawa kawayen wanda akai wa, suma su sa a ransu dole sai an yi musu irin wannan, kuma yana janyo matsala babba a cikin zaman aure.
Safyanu Auwal Garba:
Tabbacin gaskiya da yawan matasa akwai wadanda suke kure rayuwar su, sannan su matse kansu don birge wacce za su aure ta hanyar yin lefe da yawa, ko abin da yayi kama da haka, sai dai ta wani bangaren daban kuma akan samu masu yin lefe wanda sun isa su yi shi dai-dai da yadda suke komai yawansa, amma mostly karya ya fi yawa. Amfani yin lefe da yawa mun sauka kan wannan manufa da yawan masu yin shi suna yi ne domin ko da mace ta shiga gidansu ta dade ba tare da ta bukaci a yi mata wani sabon kaya ba (suttura), duba da yanayi da ya dauka na hidima wanda da yawa take kai ga ta ba uwar dukiya (jarin da ake juyawa) ba ma iya cinye riba ba, amma a irin tafiyar da ake yanzu a ganina babu wani alfanu sai karya kawai a ciki. Yana da ga abubuwa da yawan lefe yake haifarwa; Akwai na can-canta da isa, akwai kuma na karya da daga kai indan bai kai ba. Can-cantar yin lefe da yawa; a) Tabbas! yana kara dankon soyayya da kauna, domin kyautatawa yana kara hakan. b) Yana ba da damar kulawa da juna da gaske sakamakon rayuwa mai kyau da aka ginawa juna tun a samartaka da ‘yan matanci. Karya a cikin lefe da yawa; a) Mutuwar aure matukar cikin karya aka shirya shi. b) Raini tsakanin ma’aurata. c) Matsaltsalu mabambanta sakamakon haka. Lefe yana da mahimmaci a rayuwar aure musamman idan mukai duba da yadda zamani ya zo tsare-tsare amma wadanda suke dai-dai da addininmu, matukar ba su kauce masa ba, amma idan ya kasance akwai son zuciya ko karye a ciki ya kan zama haramtacce ko abu mara kyau a rayuwa ma baki daya. Wannan a takaice kenan, Allah ya datar da mu ya ba mu rayuwa mai albarka ya hada mu da abokan rayuwa na gari wanda suke sonmu dan Allah da manzansa (sallal lahu alaihi wasallama).
Abba Abubakar Yakubu, daga Jos (Shugaban Kungiyar Jos Writers Club):
Masu hali ne ke haifar da tsadar Rayuwa; Game da tattaunawar da ake yi wannan mako, a gaskiya ni a ganina, masu hali ko masu hannu da shuni da ke cikin al’umma su ne suke haifar da wannan matsalar karyar yin lefe mai yawa, don bambanta kansu da masu karamin karfi ko kuma saboda gasa a tsakaninsu. Amma ba shi da alaka da soyayyar da ango ko iyayen ango ke yi wa amarya, ko kuma a sa ran yawan lefen da aka yi zai sa amarya ta kara nuna wa angonta soyayya bayan aure. Fahimtar juna a tsakanin masoya ko tsantsar soyayya ta zuciya ta tsakani da Allah ce ke bambanta yadda zamantakewar ma’aurata za ta kasance, musamman masu sabon aure, ba yawan dukiyar da aka kashe ba. Wannan yana burge mutane ‘yan taya murna ne da masu yayatawa a zaurukan sada zumunta, ko kuma su ango da amaryar su sa rai da burge abokai da kawayensu, don a rika kururuta dukiyar da aka kashe ko kuma a goge raini tsakanin wannan iyalin da wancan. Yin lefe yana da kyau, domin na farko kyautatawa ce tsakanin mai so da wadda ake so, yana kuma kara kwarjinin amarya a gidan aurenta, yadda zai zama ta shiga gidan mijinta da sababbin kaya, ba wanda ta saba da su ba. Kuma sau da dama wannan lefen wasu iyayen amarya ke kallo, su kara yawan kayan za ki ko garar da za su raka amarya da su, bisa tunanin ai angon ya yi kokari shi ma bari a saka masa da abin da zai ji dadi. Sai dai hakan bai kamata ya zama ma’aunin da iyaye suke dubawa don yi wa ‘yar su kayan daki ko gara ba, matukar sun amince da halayen wanda zai auri ‘yar su da kuma addinin sa. Idan ina da hali, zan yi duk abin da ya dace in ga na kyautata lefen da zan yi wa matar da zan aura. Amma ba zan jefa kaina a bashi ko wani kunci ba, don yin abin da na san ba ni da halin yi. Zan mayar da hankali wajen nunawa matata soyayya da kulawa yadda ya kamata, ko da arziki ko babu!.
Salis Aliyu daga Jihar Kano:
Ka takure kanka wajen lefe ba shi da amfani ko kadan, zaman lafiya da kwanciyar hankali ya fi yawan lefe. Yawan lefe ba shi ne ke kara dankon soyayya ba, sai dai daman can akwai soyayyar sai dai kuma in ba ta Allah ba ce daman can. Lefe yana da matukar mahimmanci domin ai sutura ce kuma daman ko baka yi ba ai za ka yi mata dinki ko a gidanka. Ina da ra’ayin yi ma wadda zan aura lefe domin daman zan mata ko a gidana ne, amman batun mai yawa ko kadan wannan Allah ne ya san yadda abin zai zo domin komai ai kamawa take.
Fatima Ya’u daga Jihar Kano:
Gaskiya a yanzu zamanin da ake ciki idan ba a yi maka lefe da yawa ba toh gani ake yi kamar sadaka aka bayar da kai, to dai shi yawan lefe idan an yi aure baya kara komai sai dai zaman lafiya. Lefe yana da matukar mahimman a rayuwar aure. Eh! zan iya saboda na san inda na je. Shawarata ga maza shi ne su daina yi wa mata karyar lefe saboda zama ne ba na karewa ba, dan haka babu abin da karya za ta anfana muku.
Maryam Nura:
Eh! zan iya auren namijin da bai mun lefe ba, Maza su daina yin karyar lefe dan lefe ba shi ne albarkar aure ba. Mahimmancin lefe shi ne; kamar yadda aka ce namiji shi ne cinta, sutararta, toh ita suturar ita ce ya fara yinta tun a waje, saboda wasu Mazan idan suka ga ka riga ka shiga ba lallai su rinka dinka maka kaya ba, shiyasa ake fara kwato ‘yanci anan gurin, sai aka kwato lefe, sabida idan ya yi mata lefen nan sai a shekara bai mata dinki ba, amma ba wani mahimmanci ne da shi ba a addinance, tunda in ta je gidanshi ma dai dole zai mata sutura, sabida nauyinta yana kansa. Lefe ba ya wani kara dankon soyayya, amma wasu matan marasa tunani suna iya soke auren sabida karancin lefe, amma baya sawa aure ya dore ko ya kara dankon soyayya.
Maryam Muhammad daga kasar Nijer:
Na farko dai lefe yanada kyau sabida da yawan ‘yan mata idan za su yi aure sukan yi kyauta da kayen sakawar su to kinga wannan lefen zai iya taimakawa gurin samun sababbin kaya. Yana sa a tuna baya ne, kuma ai duk sanda mutum ya dauko kayan lefe zai saka zai ji soyaya ta karu a zuciyarsa. Mahimmacinsa dai shi ne yana taimakawa gurin samar da karin kayan sakawa kuma ai ya zama tamkar al’ada ne. Eh! koma ya ya kawo Allah dai ya sanya albarka a cikin auren. Maza su daina karya idan ba ka da shi ai bai zama dole ba ka tilasta wa kanka abun da ba ka da shi, sabida yin karyar haka zai iya janyo mutuwar aure.
Muhammad Zayyan
Gaskiya ma fi akasarin wasu mazan karya ce take sawa su yi lefe dozin, amma wasu kuma wadata ce take sawa hakan, amma duk da hakan lefe dozin ya zama hauka wallahi, Ni dai gaskiya a tawa fahimtar lefe bai zama dole ba, amma dai zan sake.
Aisha Mustapha Musa (Ayoushat Make Ober) Jihar Kano Gwammaja:
Abu na farko ba a ce babu kyau ba, kyautatawa ce amma saboda ke ma in kin samu za ki bayar, wanda kika bawa zai ji dadi tamkar ke, yanada kyau sosai ma za ta ga dai wannan kaya daga hannunsa ya fito za ka ji dadi, za ta ji ita ma hakan zai kara dankon soyayya a tsakaninku, mahimancin yinsa shi ne ka dauke ta da daraja tun anan ka nuna za ka ciyar da Ita, za ka shayar da ita, za ka tufatar da ita, ,ba zan iya auran namijin da bai min lefe ba, yayi min komai kankantar ta fi bai yi ba. Shawarata anan ita ce; duk Namijin da ya yi wa Maca karya akan yana da shi kuma ba shi da shi auransu babu inda zai je, saboda shi aure an fi san a dakko shi ta hanya ta gaskiya, amma tun farko ka dauko karya.