Gwamnatin Tarayya na shirin rage hauhawar farashi daga kashi 34 a shekarar 2024 zuwa 15 a shekarar 2025.Â
Wannan na daga cikin kasafin kudi na shekarar 2025 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokokin kasar.
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tsawaita Kasafin 2024 Zuwa Watanni 6 – Akpabio
- Yaƙin Gaza Ya Kusan Zuwa Ƙarshe – Amurka
Gwamnatin na son rage hauhawar farashi ta hanyar aiwatar da gyare-gyare a tattalin arziki, kara yawan samar da mai, da inganta fitar da kayayyakin gona.
Wadannan matakai na nufin rage farashin kayayyaki, daga darajar Naira, da kuma kara adadin ajiyar kudaden waje.
Inganta tsaro na daga cikin muhimman matakan.
Gyaran man fetur shi ma yana daga cikin muhimman dabarun da gwamnatin ta shirya yi.
Gwamnatin kuma na shirin kara yawan samar da man fetur, wanda zai taimaka wajen samun karin kudaden shiga da kuma tallafawa ajiyar kudaden waje.
Wannan zai taimaka wajen daidaita canjin Naira da rage hauhawar farashi.
Kasafin kudin na da nufin nemo karin zuba jari daga kasashen waje, wanda zai inganta wadatar kudaden waje, rage matsin lamba a kan darajar canjin kudi, da kuma rage farashin kayayyakin da ake shigo da su.
Gwamnatin tana fatan cewa wadannan matakai za su rage hauhawar farashi zuwa 15 a shekarar 2025, ta yadda zai inganta rayuwar al’umma da kuma bunkasa tattalin arziki.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa yanayin kasuwar duniya da aiwatar da manufofin cikin gida zai taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri.