Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gargaɗi gwamnatin tarayya cewa, kada a yi sakaci Birai da Macizai su Haɗiye dala biliyan 1.07 da aka ware wa fannin lafiya a kasafin kudin 2025.
Atiku a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ya bukaci a samar da hanyoyin da za a tabbatar da an yi amfani da kudaden wajen inganta harkokin kiwon lafiya maimakon karkatar da su, ta yadda za su zama cikin lalube.
- Ba Laifi A Binciki Gwamnatin Mahaifina, Amma A Yi Da Zuciya Ɗaya – Bello El-Rufai
- Gwamna Zulum Ya Mika Sandar Mulki Ga Sabon Shehun Dikwa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya yi nuni da cewa, bai kamata a ce dabbobi irin su Macizai da Birai ne ke da alhakin bacewar kudaden jama’a ba, bai kamata irin haka ta faru a kudaden kasafin kiwon lafiya ba.
Ya kuma yi kira da a samar da tsari na gaskiya da rikon amana don bin diddigin yadda ake kashe kudaden da aka ware domin amfanin jama’a.