A wani magidancin manomi na wani kauye a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa na jiran a debo su a tafi da su. An kintsa wasu wanda za a ajiye a teburin cin abinci na mutanen wurare daban daban.
Wannan kauye sunansa Diliubu, wanda aka fi sani da babban tushen kayan lambu na biranen Beijing da Tianjin na kasar Sin, zai samar da kayayyakin amfanin gona ga manyan biranen kasar a lokacin bikin bazara dake tafe, ko kuma bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.
- Xi Ya Mika Gaisuwar Bikin Bazara Ga Dukkan Sinawa
- Tabbas Philippines Ba Za Ta Cimma Yunkurinta Na Kafa “Karamar Da’Ira” A Tekun Kudancin Sin Ba
A yayin da kauyen ya kasance zangon farko na rangadin kwanaki biyu da ya yi a birnin Tianjin, shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Alhamis ya ziyarci kauyukan da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a lokacin zafin da ya gabata, ya kuma samu labarin farfadowar ayyukan noman a yankin.
Shekaru da dama, shugaba Xi na kasar Sin yana da al’adar ziyartar talakawa, musamman ma marasa galihu, gabanin bikin bazara, hutu mafi muhimmanci a kalandar kasar Sin, wanda ya fado a ranar 10 ga watan Fabrairun wannan shekara, bikin wani lokaci da ake kasancewa tare da iyali a bisa al’ada.
Bugu da kari, a jiya Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin sojin kasar, ya ziyarci sojojin da aka jibge a birnin Tianjin dake arewacin kasasr Sin a gabanin Bikin Bazarar ko sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.
Xi ya mika gaisuwar bikin ga rundunar ‘yantar da jama’a da na rundunar ‘yan sandan kasar, da fararen hula da ke aiki tare da sojoji, da ’yan sa kai da na dakarun kiyaye zaman lafiya, a madadin kwamitin koli na JKS da kwamitin sojin kasar. (Muhammed Yahaya)