Kasar Ingila wadda ke rike da kambun kofin zakarun Turai na mata ta fitar da Nijeriya daga gasar kofin Duniya ta mata da ake bugawa a kasar Australia.
An shafe shafe mintun 120 ana fafatawa tsakanin Super Falcons na Nijeriya da kuma 3 Lions na kasar Ingila kafin kawo karshen wasan.
Wasan ya tashi babu ci abinda ya sa aka kai zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga.
‘Yan wasan Nijeriya Micheale Alozie Da Desire Oparanozie ne suka barar da damarsu ta zura kwallo a raga.
Yayinda yar kwallon Ingila Chloe Kelly ta jefa kwallon da ta yi sanadiyar fitar da Nijeriya daga gasar.
Tunda farko dai Super Falcons sun samu nasarar akan masu masaukin baki Australia da ci 3-2 a wasan zagaye na 16 na gasar kofin Duniya.