Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta ce an yankema wasu Mata biyu masu rajin kare ‘yancin masu luwadi da madigo hukuncin kisa a Kasar Iran.
Matan biyu sune, Zahra Sediqi Hamedai da Elham Chubdar, Kungiyar mai suna Hengaw ta ce wata kotu ce ta zargesu da laifin yada ayyukan ‘yan luwadi da Addinin Kiristanci da kuma tattaunawa da kafafen yada labaran da ke adawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.
An kuma zargi matan da laifin cin hanci da rashawa – wanda hukuncin hakan ke zamantowa kisa a Kasar ta Iran.
Dama tuni Matan na tsare a gidan yari a birnin Urmia, inda wata Kotu ta yanke musu hukuncin Kisan.