ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Bincike Kan Kutsen Yanar Gizo Da NSA Ta Amurka Ta Yiwa Jami’ar NPU Ta Sin

by CMG Hausa
4 years ago
NPU

A yau ne, hukumar daidaita mummunar manhajar da ta bata kamfuta ta kasar Sin da kuma kamfanin Qihoo 360 na kasar Sin, suka gabatar da rahotannin binciken batun kutsen yanar gizo da aka yiwa jami’ar koyon ilmin masana’antu ta yankin arewa maso yammacin kasar Sin wato NPU. 

Rahotannin ya shaida cewa, ofishin kula da aikin kai harin musamman wato TAO dake karkashin jagorancin hukumar kula da tsaron kasar Amurka wato NSA, ya yi amfani da hanyoyi fiye da 40 wajen yi wa yanar gizon NPU kutse da kuma leken asiri a fannonin tsarin na’urori masu amfani da yanar gizo, da bayanan yanar gizo, da abubuwan dake shafar aikin sarrafa tsarin yanar gizo da sauransu.

  • Rukunin Sojoji Injiniyoyi Na Tawagar Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Ta Sin Dake Congo Kinshasa Ya Kammla Aikin Gyara Titi A Kasar

Bisa rahotannin binciken da aka gabatar, an ce, hukumar NSA ta shirya sosai na dogon lokaci, don boye ayyukan da ta yi na kutsen yanar gizon NPU da sauran tsarin sadarwa na kasar Sin.

ADVERTISEMENT

Ofishin TAO ya yi amfani da na’urorin kamfuta guda 54 wajen yin kutsen, wadanda suke cikin kasashe 17 kamar Japan, da Koriya ta Kudu, da Sweden, da Poland, da Ukraine da sauransu, kashi 70 cikin dari daga cikinsu kuma, suna makwabtaka da kasar Sin.

Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a yau cewa, mummunan aikin na kasar Amurka ya kawo babbar illa ga tsaron kasar Sin da tsaron bayanan sadarwa na jama’ar kasar, kuma Sin din ta yi tir da hakan, tare da bukatar Amurka da ta yi bayani game da batun da kuma dakatar da irin wannan mugun aiki. (Zainab)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

NPU
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Iran Ta Yanke Wa ‘Yan Madigo Biyu Hukuncin Kisa

Kasar Iran Ta Yanke Wa 'Yan Madigo Biyu Hukuncin Kisa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.