Idan ana son ambatar sunayen kasashen da ke neman tabbatar da ci gaban kasashe daban daban na bai daya a duniya, to, ba za a rasa kasar Sin ba. Shugaban kasar, Xi Jinping, ya jaddada sau da dama cewa, “Ba zai yiwu a samu walwalar duniya da kwanciyar hankali bisa tushen mai kudi na kara samun kudi, yayin da mara kudi ke kara faduwa cikin kangin talauci ba.”
Don daidaita yanayin rashin ci gaba dake damun dimbin kasashe, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya ta Global Development Initiative (GDI) shekaru 5 da suka gabata. Kana a kwanan baya, shugaban ya aika da sako ga taron manyan jami’ai kan cika shekaru 5 da gabatar da shawarar GDI da ya gudana a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, inda ya sake nanata cewa, ci gaban tattalin arziki tushe ne na jin dadin rayuwar jama’a.
Shawarar GDI ta kunshi bayanai masu nasaba da fannoni 6, wato dora matukar muhimmanci kan neman ci gaban tattalin arziki, da kokarin inganta rayuwar jama’a, da rage gibin dake tsakanin kasashe masu tasowa da masu sukuni, da amfani da fasahohin zamani don amfanar da al’ummun kasashe daban daban, da sauya salon tattalin arziki zuwa mai kare muhalli, da kokarin aiwatar da nagartattun manufofin da aka tsara.
Cikin shekaru 5 da suka wuce, shawarar GDI ta samu karbuwa sosai a duniya. Zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 130 sun goyi bayan shawarar, kana kasashe kusan 100 sun kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa tare da kasar Sin. Kana a bisa tsare-tsare masu alaka da shawarar, an ware kudin da yawansa ya kai fiye da dala biliyan 23, wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa masu amfanar da jama’a fiye da 1800, da horar da mutane masu neman koyon fasahohi fiye da dubu 200, da taimaka wa yunkurin raya tattalin arziki a kasashe fiye da 120.
A kasar Najeriya ma ana iya ganin amfanin shawarar GDI. Wani bayanin da jaridar The Guardian ta kasar Najeriya ta watsa a kwanan baya ya ambata cewa, kasar Sin ta aiwatar da ayyuka da dama masu amfanawa jama’a a Najeriya, misali haka rijiyoyi, da kafa dakunan karatu da ake koyar da fasahohin dijital, da yayata fasahar noman shinkafar da aka tagwaita irinta, da samar da tallafin na’urorin da ake bukata a asibitoci, da dai sauransu. Kana a cikin ayyukan, aikin gina gandun noman laimar kwado ya janyo hankali sosai, har ma ma’aikatar aikin gona ta kasar Najeriya ta bayyana shi a matsayin nasarar da aka samu a fannin kokarin neman samun isasshen abinci.
Kasar Sin ta nuna wa duniya ra’ayinta na tabbatar da ci gaban kasashe daban daban, ta hanyar gabatar da shawarar GDI shekaru 5 da suka wuce, wadda ta yi matukar kokarin aiwatarwa daga bisani. Hakan ya shaida cewa, kasar Sin aminiya ce ga duk wata kasa dake neman raya tattalin arzikinta. (Bello Wang)














