Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, bisa zargin kashe kishiyarta, Jamila Adamu, yayin wani rikicin ciki a jerin Gidajen Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Habib ya ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 4:05 na yamma, bayan sashen ’yansanda na C-Division da ke Bauchi ya samu rahoton rikicin tsakanin matan biyu.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa Hauwa’u, wadda ita ce matar aure ta biyu, ta ɗauki wata taɓarya, inda ake zargin ta buga wa Jamila mai shekaru 43 a goshi, lamarin da ya sa ta faɗi a sume.
Jami’in ya kara da cewa, bayan garzayawa da ita Asibitin kwararru da ke Bauchi, Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarta nan take.














