Kasar Sin ta ce bai kamata kasar Japan ta dauki rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta fitar a matsayin izinin zubar da dagwalon nukiliya cikin tekun ba, tana mai bukatar Japan din ta hada hannu da hukumar IAEA wajen samar da wani tsarin sa ido na kasa da kasa, mai dogon zango.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan a lokacin da aka nemi ya yi tsokaci kan rahoton, wanda ya yi amana shirin Japan na zuba dagwalon nukiliya cikin teku ya dace da matakan aminci na kasa da kasa. Yana mai cewa, IAEA za ta dauki lokaci mai tsawo tana sa ido kan ayyukan Japan.
A cewar kakakin, an gano rahoton ya gaza bayyana cikakken ra’ayoyin masanan da suka nazarci shirin, haka kuma ba a sanar da dukkanin masanan sakamakon nazarin ba.
Yana mai cewa, kasar Sin na takaicin gaggawar da aka yi wajen fitar da rahoton.
Bugu da kari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya maida martani kan rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA, na tantance aikin zubar da dagwalon ruwan nukiliyar kasar Japan cikin teku, inda ya jaddada cewa, bai kamata Japan ta dauki rahoton a matsayin izinin zubar da dagwalon nukiliya cikin tekun ba.
Wang ya nuna cewa, rahoton ba ya shaida amincin shirin Japan, na juye dagwalon ruwan nukiliyar ta cikin teku, kana kuma, ba zai iya tabbatar da tsaron aikin ba. Jami’in ya jaddada cewa, juye dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, zai illata babbar moriyar kasa da kasa, don haka bai kamata a kuskure fahimtar hakan ba.
Game da batun, mai fashin baki yana mai cewa, bayan da ya duba rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA ya fitar jiya Talata 4 ga wata, wanda ya yi duba kan yunkurin kasar Japan na zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku, babban jami’in kungiyar masu aikin su ta jihar Miyagi-ken ta kasar, Terazawa Haruhiko ya nuna damuwa sosai. Kamar yadda yake nuna damuwa kan hakan, jama’ar kasar Japan da dama suna ganin cewa, abun da rahoton ya bayyana, cewa wai shirin juye dagwalon ruwan nukiliya cikin teku na Japan, ya dace da ma’aunin tsaro na kasa da kasa, ba mai gamsarwa ba ne. Har ma kungiyoyin da ba na gwamnati ba da dama a kasar Koriya ta Kudu sun ce, bai dace rahoton ya zama dalilin Japan na juye dagwalon ruwan nukiliya cikin tekun ba.
Saboda rahoton bai bayyana ra’ayoyin dukkan kwararrun da suka halarci aikin tantancewa ba, kuma sakamakon rahoton bai samu amincewa ta bai daya daga dukkan kwararrun ba.
Idan aka dubi ayyukan da kasar Japan take yi kwanan nan, akwai abubuwan shakku sosai a ciki. Mu dauki kasafin kudin hukumar farfado da kasar ta Japan na shekara ta 2021 a matsayin misali, kasafin kudin da ya shafi shawo kan tasirin hadarin makamashin nukiliya a tashar Fukushima ya karu zuwa kudin Japan Yen biliyan 2, wanda ya ninka har sau 4 idan aka kwatanta da na shekara ta 2020. Haka kuma, kafafen watsa labaran Koriya ta Kudu sun ce, kafin hukumar IAEA ta bullo da rahoton, gwamnatin Japan ta riga ta samu daftarin sa, har ma ta gabatar da ra’ayoyin gyaran shi.
Bugu da kari, an ce, jami’an gwamnatin Japan sun baiwa jami’an hukumar IAEA kyautar kudade da yawansu ya zarce EURO miliyan 1. Idan da gaske ne hakan, to, ina dalilin da ya sa gwamnatin Japan ta kashe wadannan kudade tare da yin irin wannan kokari?
Ba za’a iya amincewa da yunkurin gwamnatin Japan, na zubar da dagwalon ruwan nukiliya sama da ton miliyan 1 zuwa tekun Pasifik a cikin nan da shekaru 30 masu zuwa ba. Zabin Japan na zubar da shi kai-tsaye domin cimma muradun kanta, kawai haifar da hadari ne za ta yi, ga daukacin al’ummun duniya. (Masu Fassarawa: Fa’iza Mustapha, Murtala Zhang)