A jiya Laraba, kasar Sin da Brazil sun yanke shawarar daga matsayin alakarsu zuwa matakin zama al’umma mai makomar bai daya domin samun duniya mai adalci da dorewa.
An yanke shawarar haka ne a yayin ganawar Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kuma takwaransa na kasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva. Shugaba dai Xi ya ziyarci aiki ne a kasar bayan ya halarci taron kolin kungiyar G20 karo na 19 da ya gudana a birnin Rio de Janeiro.
- Tsohon Sakataren FEDECO, Ahmadu Kurfi, Ya Rasu Yana Da Shekaru 93
- Wakilin Sin Ya Ce Abin Kunya Ne Hawa Kujerar Na Ki Da Amurka Ta Yi A Kan Kudurin Tsagaita Wuta A Gaza
Xi ya ce, alakar kasar Sin da Brazil ta kara kulluwa sosai fiye da kowane lokaci a tarihi wanda hakan ba kawai ya kara inganta jin dadin al’ummomin kasashen biyu ba ne, har ila yau ya kara kare muradu na bai daya na kasashe masu samun ci gaba, da kara karfin fada-a-ji na kasashe masu tasowa da kuma bayar da gagarumar gudunmawa ga wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Xi ya kuma nunar da cewa kasar Sin da Brazil sun kuma yanke shawarar samar da kawanceceniyar aiki a tsakanin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) da kuma matakan bunkasa ci gaban kasar Brazil.
Ya jinjina wa shawarar daga matsayin alakar kasashen nasu da kuma tsara tafiyar da matakan ci gaban kasashen kafada-da-kafada a matsayin wani sabon tarihi na huldar ci gaban kasashe wadda ke nuna yanayin kyakkyawar dadaddiyar alakar Sin da Brazil, da cikar burikan al’ummominsu, da kara wa aikin zamanantar da kasashen biyu kuzari da goyon baya, kana da nuna matsayarsu ta hada gwiwa don kare adalci a tsakanin kasashen duniya da kuma daukaka ci gaban duniya na bai daya.
Bayan kammala taron a tsakanin shugabannin kasashen biyu, sun shaida yadda aka rattaba hannu a takardun hadin gwiwa daban daban da kuma gabatar da jawabi ga ’yan jarida a tare. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere).