Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya musanta kalaman na ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi na cewa, “kasashen da ke goyon bayan kasar Rasha ko shakka babu za su shiga cikin tarihin da bai dace ba.”
Wang ya jaddada cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana yanke nata hukunci bisa hakikanin shaidu na tarihi da daidai kan batun da ya shafi kasar Ukraine. Haka kuma, a ko da yaushe kasar Sin tana tare da bangaren tabbatar da zaman lafiya da adalci.
Wang Wenbin ya kara da cewa, a daidai lokacin da Amurka ta karya alkawuran da ta dauka da ma kara fadada kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashi, lamarin da ya cusa nahiyar Turai cikin rikici da tashe-tashen hankula, kasar Sin ta yi kira ne da a kafa tsarin tsaro mai daidaito, da inganci da kuma dorewa a nahiyar Turai.
A yayin da Amurka ke ikirarin kare rayukan al’ummar Ukraine har zuwa karshe, ita kuwa kasar Sin na kara karfafa shawarwarin zaman lafiya, tana mai nuni da cewa, ya kamata kasashen duniya su goyi bayan bangarorin biyu wajen yin shawarwari, amma ba yaki ba.
Haka kuma, a yayin da Amurka ke ci gaba da kakaba takunkumi da matsa lamba, kasar Sin tana adawa da siyasantarwa, ko ba da makamai ko amfani da makamai kan tattalin arzikin duniya, tana mai jaddada cewa, bai kamata a lalata nasarorin hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa da aka samu a lokaci guda ba. Bugu da kari, bai kamata jama’ar sauran kasashe, su dandana akubar tasirin hakan ba. Duniya za ta yanke shawara kan wanda ke bangare na gaskiya.(Ibrahim)