• Leadership Hausa
Thursday, September 21, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Tinubu Ya Zabi Kabir Ibrahim Masari Daga Katsina A Matsayin Mataimakinsa

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar da sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin mataimakinsa a zabe mai zuwa na 2023.

by Muhammad
1 year ago
in Siyasa
0
2023: Tinubu Ya Zabi Kabir Ibrahim Masari Daga Katsina A Matsayin Mataimakinsa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Daily Trust ta rawaito cewa, Tinubu ya mika sunan Kabir Masari ne a matsayin wanda zai tsaya gabanin wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ba jam’iyyu na su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023.

  • 2023: Ban Ce Zan Dauki Mataimaki Musulmi Ba – Tinubu
  • Tun Da Nake Ban Taba Shan Kaye A Zabe Ba – Tinubu

Wasu majiyoyi daga bangaren Tinubu da Masari sun tabbatar wa Daily Trust haka a yammacin ranar Alhamis.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina kuma dan uwan ​​Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina.

Mataimaki na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya taba zama sakataren jin walwala na kasa a jam’iyya APC a lokacin Kwamared Adams Oshiomhole yana matsayin Jam’iyyar na kasa.

Labarai Masu Nasaba

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Roki Obaseki Ya Gafarce Shi

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Dan Majalisar Wakilai A Kano Ta Tabbatar Da Nasarar Kofa

Oshiomhole ya shugabanci APC daga 2018 zuwa 2020.

Abokin takarar Tinubu dan jam’iyyar PDP ne a zamanin marigayi shugaba Umaru Musa Yar’adua.

Bayan rasuwar ‘Yar’aduwa a shekarar 2010, Masari ya koma jam’iyyar (CPC), jam’iyyar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi takara a karkashinta amma ya sha kaye a zaben 2011.

Masari ya yi aiki da shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya hau mulki bayan rasuwar Yar’adua.

Gabanin zaben 2015, CPC ta ruguje tsarinta zuwa APC, Masari ya koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Wasu rahotanni na cewa Tinubu zai maye gurbin Masari kafin zabe saboda yanzu kawai ya mika sunansa ne domin ya cika wa’adin INEC.

“Tinubu yana ci gaba da tuntubar juna kan zabo abokin takararsa. Zai maye gurbin Masari da zarar an zabi wanda ya dace,” inji wata majiya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023,

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kasar Sin Ko Da Yaushe Tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Kan Batun Kasar Ukraine

Next Post

Sakon Xi Ya Karfafa Gwiwar Matasan Afrika Wajen Raya Huldar Sin Da Afrika

Related

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Roki Obaseki Ya Gafarce Shi
Labarai

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Roki Obaseki Ya Gafarce Shi

3 hours ago
Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Dan Majalisar Wakilai A Kano Ta Tabbatar Da Nasarar Kofa
Labarai

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Dan Majalisar Wakilai A Kano Ta Tabbatar Da Nasarar Kofa

2 weeks ago
Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar Kogi Ta Gabas
Manyan Labarai

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar Kogi Ta Gabas

2 weeks ago
NNPP Ta Maka Kwankwaso A Kotu Kan Zargin Yi Wa Jam’iyya Makarkashiya
Manyan Labarai

DA DUMI DUMINSA: Kotu Ta Dakatar Da Korar Kwankwaso Daga Jam’iyyar NNPP

2 weeks ago
Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar NNPP A Jihar Benue Ya Fice Daga Jam’iyyar
Manyan Labarai

Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar NNPP A Jihar Benue Ya Fice Daga Jam’iyyar

3 weeks ago
NNPP Ta Maka Kwankwaso A Kotu Kan Zargin Yi Wa Jam’iyya Makarkashiya
Manyan Labarai

NNPP Ta Maka Kwankwaso A Kotu Kan Zargin Yi Wa Jam’iyya Makarkashiya

1 month ago
Next Post
Sakon Xi Ya Karfafa Gwiwar Matasan Afrika Wajen Raya Huldar Sin Da Afrika

Sakon Xi Ya Karfafa Gwiwar Matasan Afrika Wajen Raya Huldar Sin Da Afrika

LABARAI MASU NASABA

Yawan Jarin Da Sin Ta Zuba A Ketare Daga Janairu Zuwa Agusta Ya Rika Karuwa

Yawan Jarin Da Sin Ta Zuba A Ketare Daga Janairu Zuwa Agusta Ya Rika Karuwa

September 21, 2023
Super Eagles Ta Nijeriya Ta Dawo Mataki Na 40 A Jadawalin Kasashen Da Suka Fi Iya Taka Leda A Duniya

Super Eagles Ta Nijeriya Ta Dawo Mataki Na 40 A Jadawalin Kasashen Da Suka Fi Iya Taka Leda A Duniya

September 21, 2023
Sin Ta Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Kare Mabanbantan Halittun Teku

Sin Ta Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Kare Mabanbantan Halittun Teku

September 21, 2023
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Lardin Zhejiang

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Lardin Zhejiang

September 21, 2023
Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Roki Obaseki Ya Gafarce Shi

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Shaibu Ya Roki Obaseki Ya Gafarce Shi

September 21, 2023
IPC

IPC Ta Yi Tir Da Muzguna Wa ‘Yan Jarida Yayin Daukan Rahoton Shari’ar Kujerar Gwamna A Kano

September 21, 2023
Bayan Gindaya Wa’adi: Hukumar AGIS Na Tattara Harajin Naira Biliyan Daya A Kullum 

Bayan Gindaya Wa’adi: Hukumar AGIS Na Tattara Harajin Naira Biliyan Daya A Kullum 

September 21, 2023
An Dawo Da Biyan Tallafin Man Fetur: Gwamnatin Tarayya Ta Biya Naira Biliyan 169.4 A Watan Agusta

An Dawo Da Biyan Tallafin Man Fetur: Gwamnatin Tarayya Ta Biya Naira Biliyan 169.4 A Watan Agusta

September 21, 2023
NUJ Ta Yi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Gaggauta Zakulo Wadanda Suka Yi Wa Danjarida Kisan Gilla A Zamfara

NUJ Ta Yi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Gaggauta Zakulo Wadanda Suka Yi Wa Danjarida Kisan Gilla A Zamfara

September 21, 2023
Uefa

UEFA Champions League: Real Madrid Ta Sha Da Kyar A Hannun Union Berlin

September 21, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.