Karancin makamashi matsala ce da galibin kasashen Afirka ke fuskanta, a yayin da kuma nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin sassan duniya da suke karancin karfin tinkarar sauyin yanayi, don haka, ya zama dole kasashen Afirka su bunkasa makamashi mai tsabta a wani kokari na tabbatar da dauwamammen ci gabansu.
A watan Afrilun bana, rukunin na’urori na farko ya fara samar da wutar lantarki a madatsar ruwa ta Zungeru da ke kogin Kaduna na jihar Niger ta kasar Nijeriya, tasha ce da kamfanin kasar Sin ya gina, wadda ake sa ran zata iya samar da wutar lantarki da zai biya bukatun birane biyu da girmansu ya kai kamar na babban birnin Abuja, wadda kuma za ta taimaka ga kyautata matsalar karancin wuta da ake fuskanta a kasar, da ma tabbatar da dauwamammen ci gaban kasar.
A hakika, tuni kasar Sin ta aiwatar da shirye-shirye sama da 100 a fannin samar da makamashi mai tsabta da kiyaye muhalli a kasashen Afirka. Misali a kasar Habasha, tashar Adama da ta Aysha da kamfanonin kasar Sin suka gina, wadanda ke samar da wuta ta amfani da makamashin iska, sun bunkasa makamashi mai tsabta, wadanda suka samar da tabbaci ga bunkasuwar masana’antu da ma rayuwar al’umma a kasar.
A kenya, tashar samar da wuta ta amfani da makamashin rana ta Garissa da kamfanin kasar Sin ya gina, ta kasance irinta mafi girma a gabashin Afirka, wadda tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyyata ya taba bayyana ta a matsayin wadda ta taimaka wa Kenya wajen dogara da kanta wurin samar da makamashi mai tsabta.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, ra’ayin muhimmancin kare muhalli ya yi ta kara zame wa al’ummar Sinawa jini da tsoka.
A yayin da ake kiyaye saurin bunkasuwar tattalin arziki a kasar, yawan iskar Carbon da aka fitar a kasar ma ya ragu ainun, baya ga muhallin halittu da yake dada kyautata, kasar Sin ta samu gaggarumin ci gaba ta fannin kare muhalli.
A sa’i daya kuma, kasar Sin ta yi kokarin rungumar makomar dan Adam ta bai daya, inda ta yi iyakacin kokarinta wajen samar da fasahohinta ga kasashe masu tasowa ta fuskar kiyaye muhalli. Kawo yanzu dai, kasar Sin ta samar da kudi yuan biliyan 1.2 kwatankwacin dala miliyan 165 wajen aiwatar da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa don tinkarar matsalar sauyin yanayi, baya ga kuma daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa 43 tare da kasashe masu tasowa 38, tare da horar da ma’aikatan kula da sauyin yanayi kimanin 2000 daga kasashe masu tasowa sama da 120.
Jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin a babban taron wakilanta na 20 da aka kammala kwanan nan ba da jimawa ba, ta tsara taswirar gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani, inda kuma ta jaddada cewa, “ya kamata kasar Sin ta zamani ta kasance yadda dan Adam ke zaman jituwa da muhalli”, tare da tsara ayyukan da za a sanya gaba a wannan fanni.
Ban da wannan, ta kuma yi nuni da cewa, ya kamata a rungumi makomar dan Adam ta bai daya, “a tsaya ga kiyaye muhalli, tare da sa kaimin gina kyakkyawar duniyar dan Adam mai tsabta.” Ta hakan muke iya hasashen cewa, nan da ba da jimawa ba, kasar Sin ba kawai za ta kasance mai karfi ta fannin tattalin arziki da al’adu ba, tabbas kuma za ta kasance mai kyakkyawan muhalli.
Tabbas kuma kasar za ta kara samar da gudummawarta wajen tabbatar da kyakkawar duniyar dan Adam da ma dauwamammen ci gabansu.(Mai zane:Mustapha Bulama)