Kasar Sin za ta jagoranci taro kai tsaye na farko cikin shekaru 31 tsakaninta da kasashen yankin tsakiyar Asiya da suka hada da Kazakhstan da Kyrgystan da Tajikistan da Turkmenistan da Uzbekistan, a ranakun 18 da 19 ga wata, wanda ke zaman muhimmin taro tsakanin bangarorin.
A ganina, wannan taro zai kara tabbatar da karfin kasar Sin na jagorantar kasashe masu tasowa wajen samun ci gaban da suke muradi da kuma ba su damar shiga ana damawa da su cikin harkokin kasa da kasa.
Hakika ba al’ummar kasar Sin ne kadai ke amfana da ci gaban da kasar ta samu ba, har ma da kasashe masu tasowa, inda take fito da su tare da kara sanyawa ana jin amonsu, domin in ban da kasar Sin, babu wata babbar kasa dake kokarin jan kasashe masu tasowa a jiki da zuciya daya.
Tarihi ya nuna cewa, kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka fara kulla huldar diflomasiyya da wadannan kasashe tun bayan samun ’yancin kansu, kuma tun daga lokacin ake samun kyautatuwar alaka a tsakaninsu.
Hakika hulda da kasar Sin babban tagomashi ne ga kowace kasa domin ta kasance mai tabbatar da adalci da aiwatar da dangantaka bisa girmama juna da moriyar juna, da kuma kaunar ganin an gudu tare an tsira tare. Burin kasar Sin a kullum shi ne ganin ci gaban kasashe masu tasowa, da burin ganin sun tsaya da kafarsu sun kuma nemi ci gaba ta hanyar da ta dace da su. Irin wannan ra’ayi shi ne ya dace da kyautata zaman lafiya da ci gaban duniya da ma kyautata zamantakewar al’umma.
Yayin da wasu kasashe suka dukufa wajen yin babakere da tsoma baki da neman ci da gumin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta kasance wata sabuwa kuma kyakkayawar fata ga makomar kasashe masu tasowa.
Bugu da kari, dangantakar wadannan kasashe za ta taimaka wajen kyautata zaman lafiyar yankin Asiya. Dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya, dangantaka ce ta moriyar juna bisa la’akari da hadin gwiwarsu a bangarori kamar na makamashi da fasaha da hakar ma’adinai da amfanin gona, inda kayayyakin wadannan bangarori da Sin ta shigo da su daga wadannan kasashe a bara, suka kasance mafi yawa, haka kuma su ne suka fi sayen kayayyakin laturoni da injuna daga kasar Sin.
Lamarin da ke nuna cewa, taron dake karatowa, zai kara bunkasa kyakkyawar dangantakar dake akwai tsakaninsu, tare da samar da karin sabbin damarmaki da ci gaban tattalin arziki. (Fa’iza Mustapha)