Akalla fasinjoji 20 ne suka kone kurmus a ranar Juma’a a wani hatsari da ya faru a mahadar Maya zuwa Lanlate da ke Karamar aramar Hukumar Ibarapa ta Gabas a Jihar Oyo.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa lamarin ya hada da wata motar haya kirar bas da wata mota kirar Sienna.
- Kasar Sin Muhimmiyar Abokiyar Hulda Ce Da Afrika Za Ta Iya Hada Hannu Da Ita Wajen Yaki Da Yunwa
- Ko Talakawa Na Amfana Da Yawaitar Sauya Shekar ’Yan Siyasa?
NAN ta kuma tattaro cewa motocin guda biyu na tafiya ne ta gaba da gaba, inda suka yi karo da juna, inda motocin suka kama wuta nan take.
Wani mutum, ya ce fasinjoji 20 da lamarin ya rutsa da su sun kone ƙurmus har ba za a iya gane su ba.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, shugaban Karamar Hukumar Ibarapa ta Gabas, Gbenga Obalowo, ya ce shi ne ya jagoranci tawagar ceto zuwa inda hatsarin ya faru.
Ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin.
Sai dai kuma ba a samu jin ta bakin kwamandan hukumar kiyaye hadura (FRSC) na Jihar Oyo, Joshua Adekanye ba, inda bai amsa kiran waya da a ka yi masa ba.