Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun ya nanata cewa, wajibi ne a yi adawa da duk wani yunkuri na tilasta sakewa jama’ar Falasdinu matsuguni tare kuma daukar batun dakatar da bude wuta a Zirin Gaza nan take, a matsayin mafi muhimmanci a yanzu.
Zhang Jun ya bayyana haka ne a jiya, yayin wani taron Kwamitin Sulhu na MDD da Aljeriya ta nemi a gudanar, kan batun tilasta sakewa fararen hula na Zirin Gaza matsuguni.
- Gwamnatin Zimbabwe Ta Yabawa Ci Gaban Da Ake Samu A Masana’antar Samar Da Karafa Da Sin Ta Zubawa Jari
- Amurka Ta Lalata Manufarta Ta Fadin Albarkacin Baki Wajen Watsa Labarai
A cewar wakilin na Sin, dakatar da bude wuta nan take ya zama wata muhimmiyar kira daga kasa da kasa, amma wata mambar dindindin a Kwmaitin Sulhun ta ki amincewa da matsayar da kwamitin ya cimma bisa wasu dalilai da dama, wadanda suka ci karo da tsarin kasa da kasa na tabbatar da adalci da gaskiya, har ma da raina ikon kwamitin sulhun.
Ya kara da cewa, wasu kan yi ta kira da a kare hakkin bil adama da magance kisan kiyashi, amma kuma bayan aukuwar rikicin Gaza, sai suka zama kurame suka juya baya. Wannan a cewarsa, nuna fuska biyu ce. Yana mai cewa dole ne a yi watsi da duk wani nau’i na tsoma baki, a dauki kwakkwaran mataki domin yayyafawa rikicin ruwa da ma ceton rayuka.
Bugu da kari, Zhang Jun ya bayyana cewa, tilas ne a yi adawa da yunkurin tilastawa mutanen Falasdinu sauya matsuguni. Ya ce yanzu haka, an takaita damar shigar da kayayyakin agaji, kuma cututtuka da yunwa na karuwa a Zirin, yayin da yanayin rayuwar yau da kullum ke gab da tabarbarewa baki daya. (Fa’iza Mustapha)