Ma’aikatar harkokin wajen Kasar Sin ta mayar da martani da Amurka, inda ta ce kasar ba ta gudu ko tsoron takara bisa adalci, amma tana adawa da yadda Amurka ke daukar dangantakarsu a matsayin ta abokan takara.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Laraba, inda ta mayar da martani ga furucin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi game da kasar Sin, yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin kasar a jiya.
A cewar Joe Biden, takara kasarsa take nema amma ba rikci ba. Ya kuma ce jarin da Amurka ta zuba a kasashe kawayenta da fannonin soji da ci gaban fasahohi, na nufin Amurka na kan wani matsayi mafi karfi cikin gomman shekaru, na takara da kasar Sin da ma kare muradunta.
A cewar Mao Ning, har kullum, Sin tana da yakinin cewa dangantakarta da Amurka ba na cin nasara daga faduwar wani bangare ba ne. Ta ce nasarorin Sin da Amurka, sun kasance damarmakin samun ci gaba ga juna amma ba kalubale ba, kuma daukacin duniya za su goyi bayan samun ci gaba da zaman lafiya a Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)