Tsohon mataimakin firaministan kasar Pakistan Zafar Mahmood, ya taba bayyana cewa, “A cikin yanayi na rashin tabbas da ake fuskanta a duniyarmu, za a iya dogaro da kasar Sin, saboda ta kan cika dukkan alkawuran da ta dauka.” Yanzu haka an samu karin fahimta game da wannan tsokaci na sa, bayan da aka saurari maganganu da ministan harkokin wajen kasar Sin ya fada, a taron manema labaru da ya gudana, a gefen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, a jiya Juma’a.
Cikin awa 1 da rabi na gudanar da taron, ministan wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi cikakken bayani kan wasu batutuwa fiye da 20, wadanda suka shafi huldar Sin da sauran kasashe, da batutuwan shiyyoyi dake jan hankalin al’ummun duniya, da tsarin kula da al’amuran duniya, da dai makamantansu.
- Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet
- Aikin Noma Ya Ragu Da Kashi 1.8 A Zango Na Hudu A Shekarar 2024
Inda babban jami’in Sin ya ambaci batun kare zaman lafiya har karo 30. Saboda kasar tana tsayawa kan turbar neman raya kasa, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kana har kullum tana kokarin kare adalci a al’amuran kasa da kasa, don haifar da wani yanayi na tabbas a duniya.
Ban da haka, jami’in ya ambaci yadda kasar Sin ta samar da yanayi mai tabbaci, ta hanyar kiyaye karuwar tattalin arziki da ta kai kaso 5%, tare da samar da gudunmowar karuwar tattalin arzikin duniya da ta kai kimanin kaso 30%.
Bisa tantance ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin raya tattalin arziki, da kare zaman lafiya da tsaro, za a fahimci rawar da kasar ke takawa, a kokarin tabbatar da makoma mai haske ga al’ummun duniya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp