Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambyar manema labarai game da halin da ake ciki a kasr Syria a yau Lahadi, inda ya bayyana cewa, Sin na maida hankali sosai kan halin da ake ciki a kasar, tare da fatan ganin maido da kwanciyar hankali da wuri a kasar. Kana kuma, gwamnatin kasar ta riga ta samar da taimako ga Sinawa dake da bukata domin su fice daga kasar, ta kuma bukaci Syria da ta dauki matakan zahiri, don tabbatar da tsaron hukumomi gami da mutanen kasar Sin dake kasar ta Syria. (Murtala Zhang)