Ma’aikatar harkokin wajen Kasar Sin ta ce kasar za ta samar da agajin gaggawa da darajarsu ta kai yuan miliyan 30, kwatankwacin dala miliyan 4.42 ga Syria.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, agajin ya hada da tallafin dala miliyan 2 da kayayyakin agaji da ake matukar bukata a inda girgizar ta auku.Haka kuma, ta ce Sin na kokarin gaggauta aiwatar da wani shiri na tallafin abinci.
A yau Laraba ne kuma shugaban kasar Turkiye, Recep Tayyip Erdogan, ya ziyarci yankin da ibtila’in ya auku, inda yawan mutanen da ta yi sanadin mutuwarsu a kasar ya kai 8,574, wanda ya kawo jimilar mamata sanadiyyar ibtila’in zuwa 11,000 idan aka hada da na Syria dake makwabtaka da kasar.
A cewar hukumomi a yankin da masu aikin ceto, mutane sama da 45,000 sun ji raunuka a kasashen biyu, sanadiyyar girgizar kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp