Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Yong ya bayyana cewa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa da dukkan bangarori a muhimman fannoni kamar na masana’antu.
Wang, wanda shi ne mataimakin shugaban babban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wacce take babbar hukumar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen bikin bude taron masana’antun duniya na shekarar 2025 da aka gudanar a lardin Anhui da ke gabashin kasar Sin.
Wang ya kara da cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa, sun bi ka’idar samun moriyar juna da hadin gwiwar samun nasara ga ko wane bangare, tare da yin amfani da dandalin taron wajen zurfafa hadin gwiwa a aikace, da ba da goyon baya mai karfi ga bunkasa masana’antun duniya.
Kazalika, Wang ya ce, a yayin da ake fuskantar wani sabon zagaye na juyin juya halin fagen kimiyya da fasaha da sauye-sauyen masana’antu, kasar Sin tana son yin aiki tare da dukkan bangarori don karfafa hadin gwiwa a muhimman fannoni kamar na masana’antu, da karya shingen da aka gitta a fannoni daban daban kamar na fasaha, da kaifin basira da harkar bayanai, da samun nasara a fasahohi masu muhimmanci, tare da cimma muradin samun ci gaba mara gurbata muhalli da rage fitar da hayaki mai gurbata yanayi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)