An samu ci gaba a fannin aikin gona mara gurbata muhalli na kasar Sin ba tare da tangarda, kamar yadda rahoton samun bunkasar aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba na kasar Sin na shekarar 2024, wanda aka gabatar a wani taro a birnin Beijing jiya Jumma’a ya nuna.
Cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin (CAAS) da kungiyar binciken ci gaban aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba ta kasar Sin ne suka fitar da rahoton.
Rahoton ya nuna cewa, an samu gagarumin ci gaba a fannoni da yawa a cikin shekarar 2024, kuma kasar Sin ta ci gaba da karfafa inganci da wadata wajen gina filayen noma masu matukar inganci, tare da karfafa kariyar muhalli da shawo kan gurbacewar filayen noma da ake da su, wanda hakan ya sa aka samu nasarar gina ko inganta fiye da hekta miliyan 5.33 na filayen noma masu matukar inganci a shekarar 2024.
Kazalika, an sami dorewar raguwar amfani da sinadarai masu cutarwa ta hanyar karfafan matakai. Rahoton ya kuma ce, yawan takin zamani da kasar Sin ta yi amfani da shi ya kai tan miliyan 49.88 a shekarar 2024, inda adadin ya ragu da kashi 5 cikin 100 daga shekarar 2020. Har ila yau, amfani da magungunan kashe kwari wajen noman amfanin gona ya kai tan 242,000, inda hakan ya nuna ci gaba da samun raguwarsa a cikin shekaru takwas a jere.
Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, amfani da kayayyakin fasahar zamani wajen noma ya ci gaba da hauhawa, inda adadin ingantattun fasahohin zamani da aka yi amfani da su wajen yin noma, da shuka, da girbi ya zarce kashi 75 cikin 100 a fadin kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp