Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin, ta ce ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 da za a tura, za su kammala aikin ginin cibiyar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wanda ya kunshi muhimman bangarori 3, wadanda suka hada da babban bangaren cibiyar na Tianhe da kumbunan dakunan gwaji na Wentian da Mengtian.
A cewar mataimakin daraktan hukumar, Lin Xiqiang, ‘yan sama jannatin za su yi aikin gina cibiyar ta sararin samaniya zuwa dakin gwaje- waje na kasar a sararin samaniya.
kasar Sin ta shirya harba kumbon Shenzhou-14 ne a gobe Lahadi, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan, inda za a tura ‘yan sama jannati 3 zuwa cibiyar ta sararin samaniya na tsawon watanni 6.
‘Yan sama jannatin na kumbon Shenzhou-14, za su yi aiki tare da takwarorinsu dake doron duniya, domin kammala hadewa da ayyukan kumbunan dakunan gwaje-gwajen biyu da babban bangaren cibiyar binciken sararin samaniya. (Fa’iza Mustapha)