Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Jumma’a cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka ta kara fahimtar yanayin batun yankin Taiwan wanda ba a wargi da shi, kana ta cika alkawuran da shugabannin Amurka suka dauka.
Lin ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na yau da kullum lokacin da aka nemi ya yi tsokaci kan wata tambaya da ‘yan jarida suka yi. An ba da rahoton cewa, a kwanan baya jagoran mahukuntan Taiwan Lai Ching-te ya halarci taron Dealbook na New York Times ta hanyar wani faifan bidiyo da aka nada kafin taron, inda ya furta wasu kalamai na ganganci game da halin da ake ciki a mashigin Taiwan.
Lin ya kara da cewa, wasu kafafen yada labarai a Amurka suna bayar da kafa ga jagoran mahukuntan Taiwan domin yada karairayi na karfafa batun “’yancin kan Taiwan” na ‘yan aware, wanda hakan ya saba wa ka’idar kasancewar Sin daya tak a duniya da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka fitar, lamarin da ke yi wa ‘yan awaren ingiza mai kantu ruwa. Kana ya ce, “tabbas Sin na matukar adawa da hakan.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)














