ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Ce Blinken Ya Yada Bayanan Karya A Cikin Jawabinsa

by Sulaiman
3 years ago

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fada Juma’ar nan cewa, jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi kan manufofin kasar Sin, ya yada labaran karya a cikinsa, ya kuma azuzuta wai “barazanar kasar Sin”, da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da kuma bata sunan manufofin cikin gida da waje na kasar Sin.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, kasar Sin ta nuna rashin amincewarta da ma adawa da kakkausar murya kan wannan jawabi.

Wang ya kara da cewa, sakatare Blinken ya bayyana cewa, Amurka ba za ta nemi rikici ko tayar da wani sabon yakin cacar baka da kasar Sin ba, kuma tana son zama lafiya da kasar Sin, za mu jira mu gani.

ADVERTISEMENT

Ya kuma lura da cewa, Amurka tana ikirarin cewa, kasar Sin ita ce babban kalubale ga tsarin kasa da kasa na dogon lokaci, Yana mai cewa, a matsayinta na kasar da ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin kasa da kasa, kullum kasar Sin tana nacewa wajen ganin cewa, ya kamata dukkan kasashe su martaba tsarin kasa da kasa tare da MDD a matsayi jagora, da tsarin kasa da kasa bisa dokokin kasa da kasa, da kuma muhimman dokokin tafiyar da dangantakar kasa da kasa bisa manufofi da ka’idojin yarjejeniyar MDD.

Daga nan Wang ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, kamata ya yi huldar dake tsakanin kowace kasa ta kasance bisa daidaito, da tuntuba, da fahimtar juna, kana ya kamata dukkan kasashe, su daidaita makomar duniya tare.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Tsarin hadin gwiwar kasashen dake yankin tekun Indiya da Pasifik da Amurka ta kaddamar wani salo ne na kafa wani gungu, wanda kuma ba zai taba yin nasara ba. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Daga Birnin Sin

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
Next Post
Sin Ba Ta Da Bukatar Adana Abinci Daga Kasuwar Kasa Da Kasa

Sin Ba Ta Da Bukatar Adana Abinci Daga Kasuwar Kasa Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.