Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, daga ranar 8 ga watan Junairu, za a soke gwajin cutar COVID-19 ga matafiyan daga ketare.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce ana shawartar masu zuwa kasar Sin daga ketare, su yi gwajin cutar sa’o’i 48 kafin lokacin tafiyarsu. Inda kuma ake shawartar wadanda gwaji ya nuna sun kamu da cutar, su jinkirta tafiyar zuwa lokacin da gwaji zai nuna ba sa dauke da ita.
Haka kuma, babu bukatar matafiya su nemi manhajar tantance yanayin cutar ta Health Code, daga ofisoshin jakadancin kasar Sin.
A cewar sanarwar, za su bayyana yanayin lafiyarsu ne a katin da za su gabatarwa jami’an kwastam.
Wadanda kuma yanayin lafiyarsu ke da matsala ko suke dauke da zazzabi, za su yi gwaji a wurin, sannan kuma za a nemi su killace kansu a gida ko su je asibiti, bisa la’akari da yanayin lafiyarsu.
A cewar sanarwar, kasar Sin za ta soke matakan takaitawa da ta sanya wa jiragen saman fasinja na kasa da kasa, inda za ta kara yawan zirga-zirgar jiragen sama bisa matakai, da inganta hanyoyin da jiragen ke bi.
Bugu da kari, kamfanonin jiragen sama za su ci gaba da fesa maganin kashe kwayoyin cuta a cikin jiragensu, kuma ana bukatar fasinjoji su sanya abin rufe fuska da baki yayin da suke cikin jirgi.
Kasar Sin za ta kara inganta tsare-tsare ga baki da ke shigowa kasar Sin don yin aiki, kasuwanci, karatu, ziyara da haduwa da dangi, da samun viza cikin sauki yadda ya kamata.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a dauki matakan tabbatar da cewa, jigilar kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa daban-daban, za su koma kamar yadda suke kafin barkewar cutar, kuma za a dawo da harkokin yawon bude ido ga ‘yan kasar Sin cikin tsari.
Wadannan sauye-sauye, sun yi daidai da ingantattun matakan rigakafin kamuwa da cutar a cikin gida, za kuma su daidaita matakan rigakafin annobar da sarrafawa tare da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da kuma sanya tafiye-tafiye tsakanin kasashe kan turba mafi dacewa, aminci, tsari da inganci.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya yi wadannan kalamai ne, a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa a Talatar nan, lokacin da aka tambaye shi game da sabbin matakan.
A kokarinta na sauya manufofinta kan cutar COVID-19, hukumar kula da lafiya ta kasar Sin ta fitar da wata sanarwa jiya Litinin, inda ta ce kasar Sin za ta sauya matakan yaki da cutar daga rukunin A zuwa rukunin B daga ranar 8 ga watan Junairu na shekarar 2023 dake tafe, tare da kuma sauyawa cutar suna daga “novel coronavirus pneumonia” wato matakin cutar mai tsanani dake shafar huhu, zuwa “novel coronavirus infection” bisa dokokin kandagarki da yaki da cutar, tare da cire ta daga jerin cututtukan dake bukatar killacewa, bisa dokokin kiwon lafiya da na killacewa na kasar.
Sawarwar da kwamitin kula da matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar, na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar a jiyan, ta ce an riga an dauki dukkan matakan da suka kamata, wadanda za su taimakwa wajen daidaita sassauta matakan, bisa dogaro da yanayin sauyawar cutar da kuma yadda ake tunkararta a kasar.
A waje daya kuma, kasar Sin ta kara daukar matakan kandagarki da dakile annobar COVID-19 a muhimman wurare, kungiyoyi da rukuninin jama’a, a daidai lokacin da kasar ta sauya matakanta na yaki da cutar COVID-19.
Muhimmiyar takardar, wadda kwamitin yaki da annobar na majalisar gudanarwar kasar ya fitar, ta lura cewa, ya kamata a kara adadin rigakafin da ake yiwa mutanen da ke zaune a wuraren kula da tsoffi da cibiyoyin jin dadin jama’a, yayin da mutane ke cikin hadarin ci gaba da shiga yanayi mai tsanani, ciki har da mutane masu shekaru 60 zuwa sama, mutanen da ke da wani rashin lafiya, da wadanda ba su da karin garkuwar jiki, aka shawarce su da su hanzarta karbar allurar dake kara karfin garkuwa. (Masu Fassarawa: Fa’iza Mustapha & Ibrahim Yaya)