Yau Jumma’a ne, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan matsayin Sin na warware matsalar Ukraine a siyasance.
Bayanin ya nuna cewa, ya kamata a girmama ikon mulkin kasa da kasa, a nuna adalci wajen bin dokokin duniya, kada a dauki ma’aunai guda biyu a kan batu guda. Ya kamata a yi watsi da tunanin yakin cacar baki. A tsagaita bude wuta nan da nan, tare da kaddamar da shawarwarin shimfida zaman lafiya, wannna ita ce hanya daya tak mai dacewa wajen warware matsalar Ukraine. Haka kuma ya kamata a warware matsalar jin kai da ake fuskanta yanzu, a mara baya ga dukkan matakan da za su taimaka wajen sassauta matsalar. Ban da wannan kuma, ya kamata a ba da kariya ga fararen hula da fursunoni, a tabbatar da tsaron tashar samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya, a magance amfani da makaman nukiliya, a tabbatar da jigilar hatsi yadda ya kamata. Haka zakila, ya kamata a daina sanya takunkumi daga gefe guda, a tabbatar da gudanar da aikin masana’antu da na samarwa yadda ya kamata, gami da ingiza aikin sake farfadowa bayan yaki.
Sannan a yau ne, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taron bainar jama’a kan hadin gwiwa da kungiyar Tarayyar Turai (EU). A jawabin da ya gabatar a yayin taron, jakadan Sin dake MDD, Dai Bing ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su gaggauta tsagaita bude wuta, da cimma daidaiton tsaro a nahiyar Turai ta hanyar tuntubar juna, da tattaunawa.
Bangaren kasar Sin ya bayyana cewa, rikicin kasar Ukraine babban kalubale ne ga tsaron kasashen Turai. Don haka Sin tana kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su gaggauta tsagaita bude wuta, kana EU, da NATO, da Amurka su ma su shiga tuntuba da tattaunawa da kasar Rasha, domin cimma daidaiton tsaro a nahiyar ta Turai.
Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan samar da zaman lafiya da tattaunawa nan da nan, da son ci gaba da taka rawar da ta dace wajen warware rikicin kasar Ukraine. (Mai fassarawa: Kande Gao, Ibrahim Yaya)