Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana matsayin kasarsa, game da samar da isasshen abinci da makamashi, inda ya gabatar da shawarar yin hadin gwiwa kan batun samar da isasshen abinci a duniya a taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20.
Na farko, shi ne tallafawa MDD wajen taka muhimmiyar rawa don daidaita lamarin.
Na biyu, daina sanya takunkuman hana fitar da abincin agajin jin kai zuwa kasashen waje da hukumar tsara shiri kan abinci ta duniya wato WFP ke yi.
Na uku, ba da damar shigar da kayayyakin amfanin gona na kasashen Rasha,da Ukraine da Belarus cikin kasuwannin duniya ba tare da wata tangarda ba.
Na hudu, ya kamata manyan kasashe masu samar da abinci da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, su ba da damar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, su kuma rage shingen ciniki da fasaha, da sarrafa makamashin abinci, ta yadda za a samu saukin karancin abinci a kasuwa.
Na biyar, ya kamata matakan gaggawa da kasashe ke dauka na cinikin abinci, su kasance na gajeren lokaci, a bayyane, a kan lokaci da kuma dacewa, tare da martaba ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya.
Na shida, tallafawa kungiyar tuntuba kan bincike game da aikin gona na kasa da kasa da kirkire-kirkire da hadin gwiwa kan kimiyya da fasahar noma tsakanin kasashe, da rage hana mu’amalar fasahohi na zamani.
Na bakwai, rage hasarar abinci da shara. Kasar Sin ta karbi bakuncin taron kasa da kasa kan hasarar abinci da shara, kuma a shirye ta ke na ganin an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron cikin hadin gwiwa.
Na takwas, taimakawa kasashe masu tasowa, su kara karfinsu na samar da abinci, adanawa da rage hasara ta fuskar jari, da fasaha da kuma kasuwa.
Wang Yi ya ce, kasar Sin sahihiyar abokiyar hadin gwiwa ce ta MDD da kasashe masu tasowa a fannin samar da abinci. Kasar Sin ta gudanar da ayyukan hadin gwiwar kasashen masu tasowa sama da 40 tare da hadin gwiwar kungiyar FAO da WFP.
Wang ya ce, kasar Sin ta kafa yankunan hadin gwiwa a fannin aikin gona tare da wasu kasashe masu tasowa, ta kuma gudanar da mu’amalar kimiyya da fasahar aikin gona tare da kasashe da yankuna sama da 140. (Ibrahim)