Tawagar dindindin ta kasar Sin a Geneva, ta gudanar da wani taro don gabatar da takardar bayani kan “Kayyade makamai, da kwance damara, da hana yaduwar makamai a sabon zamani” a jiya Laraba a “Palace of Nations” na Geneva na kasar Switzerland.
Jakadan Sin mai kula da harkokin kwance damara na Sin, Shen Jian, ya halarci taron, ya kuma yi karin haske kan bayanan da takardar ta kunsa, da mahimmancinta. Mahalarta taron fiye da 100 sun hada da wakilan dindindin a Geneva, da jakadun kwance damara, da masana na kasashe daban-daban.
Shen Jian ya bayyana cewa, a cikin takardar aka bayyana ra’ayoyi, da shawarwarin Sin game da aikin tsaron kasa, da kuma yanayin kayyade makamai a sabon zamani, kuma a karon farko, kasar ta gabatar da ra’ayinta na kayyade makamai bisa tushen adalci, da hadin gwiwa, da kokarin tabbatar da daidaito da inganci.
Bangarorin da suka halarci taron sun yaba da takardar, wadda za ta taimaka wajen fahimtar ra’ayoyi da manufofin tsaro na Sin, suna masu fatan Sin za ta kara taka rawar gani, wajen ciyar da harkar kayyade makamai a duniya gaba.(Amina Xu)














