Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin ta sanar da cewa, a daren Larabar nan ne kasar Sin ta harba kumbon Tianzhou-7 da ke dakon kaya, domin kai kayayyakin da za a yi amfani da su a tashar sararin samaniya ta Tiangong.
Roka kirar Long March-7 Y8 dauke da kumbon Tianzhou-7, ya tashi ne daga wurin harba kumbon Wenchang dake lardin Hainan a kudancin kasar Sin a ranar Larabar nan.
- Dalilin Da Ya Sa Ban Kori Emefiele A Matsayin Gwamnan CBN Ba – Buhari
- Xi Ya Taya Felix Antoine Tshisekedi Murnar Lashe Zaben Shugaban Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo
Wannan dai shi ne aikin jigilar kaya na biyu tun bayan da tashar sararin samaniyar kasar ta shiga cikin matakin aikace-aikace da ci gaba. Idan aka kwatanta da Tianzhou-6, an kara inganta karfin lodin Tianzhou-7.
Kayayyakin da ke cikin kumbon Tianzhou-7 ya hada da kayayyakin rayuwa da tufafi da abinci ga ‘yan sama jannati. (Yahaya)