Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin da ya sa bai kori Godwin Emefiele daga mukamin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) ba a lokacin da ya karbi mulki a 2015.
Idan za a tuna cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne, ya nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN bayan tsige Sanusi Lamido Sanusi a farkon shekarar 2014.
- Juyin Mulki: Rufe Iyakar Nijeriya Da Nijar Ya Jefa Arewa Cikin Tsaka Mai Wuya – Aliero
- Jiang Ying: Sin Tana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
Daga baya Jonathan ya sha kaye a zaben shugaban kasa na 2015 a hannun Buhari.
Bayan hawansa mulki a shekarar 2015, Buhari ya kori kusan dukkan masu rike da mukaman siyasa da suka yi aiki da gwamnatin Jonathan, sai dai ya bar Emefiele ya ci gaba da zama gwamnan CBN.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da kaddamar da littafin da tsohon mai ba shi shawara kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ya rubuta, mai sunan ‘Aiki Tare Da Buhari’ a ranar Talata.
Tsohon shugaban kasar ya ce tsarin sauya fasalin Naira da Emefiele ya bullo da shi ya taimaka wa kasar nan wajen gudanar da sahihin zabe a 2023.
“Ba da gangan aka bullo da karancin kudi don jefa ‘yan Nijeriya cikin wahala ba. Dimokuradiyya tana bai wa mutane damar bayyana ra’ayinsu, kuma ba mu hana su ba. Mutane sun fahimci abubuwan da suka zaba, kuma ba mu tilasta su ba.
“A zaben shugaban kasa, APC ta sha kaye a Jihar Katsina, amma kuma ta ci zaben gwamna. Watakila sun dauki abubuwa da sauki tun da farko saboda jihata ce, kuma suna tunanin za su yi nasara cikin sauki.
“Na samu Emefiele a ofis a lokacin da na zo, kuma ba ni da wata kwakkwarar hujja a kan sa game da aikata wani abu, don haka zai zama rashin adalci idan na kore shi.
“Idan kana son hukunta mutum dole ne ka samu hujja a kansa game da wani laifi da ya aikata,” in ji Buhari.
Wannan shi ne karon farko da Buhari ya ziyarci babban birnin tarayya, Abuja tun bayan sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.