Kasar Sin ta aika wani sabon tauraron dan Adam na gwaji a kan fasahar sadarwa zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Xichang da ke lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar, a ranar Alhamis.
An harba tauraron na dan Adam ne da wani roka mai suna ‘Long March-3B’ da misalin karfe 11:32 na dare agogon Beijing kuma ya shiga cikin kewayar burujin da aka tsara cikin nasara.
- Li Qiang Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabuwar Firaministar Kasar Mozambique
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
A cewar cibiyar harba tauraron na dan Adam, za a yi amfani da tauraron ne wajen harkokin sadarwa da suka shafi tauraron dan Adam, da watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin da kuma sauran ayyukan aikewa da bayanai. Kazalika, za a yi amfani da shi a matsayin dandalin gwaji da sabunta fasahohin kimiyya masu alaka da shi.
Harba tauraron na wannan karon, shi ne karo na 558 a cikin jerin manufofin amfani da rokokin na Long March. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp