Kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Xichang dake lardin Sichuan a yankin kudu maso yammacin kasar Sin Jumma’ar nan.
An harba tauraron ne samfurin APSTAR-6E ta hanyar amfani da rokar Long March-2C da karfe 2 da mintuna 10 na safe agogon Beijing na kasar Sin, kuma ya shiga falaki kamar yadda aka tsara.
Galibi ana amfani da tauraron ne wajen samar da muhimman hidimi na sadarwa ga yankin kudu maso gabashin Asiya.
Wannan shi ne karo na 460, da aka yi amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan-Adam zuwa sararin samaniya. (Ibrahim Yaya)