A yau Lahadi, kasar Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin dan Adam 14 zuwa sararin samaniya, inda aka yi amfani da rokar Long March-2D wajen harba su.
Rokar ta tashi ne daga cibiyar harba taurarin dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi, na arewacin kasar Sin da misalin karfe 11:14 na safiya.
Tuni taurarin da suka hada da Qilu-2 da Qilu-3, suka shiga falakinsu kamar yadda aka tsara.
Wannan shi ne karo na 462 da aka harba tauraron dan Adam bisa amfani da dangin rokar Long March. (Fa’iza Mustapha)