Yau Talata 21 ga wata ne kasar Sin ta kaddamar da takardar shawarar tsaron kasa da kasa a hukumance, inda aka yi karin bayani kan muhimmin tunani dangane da shawarar tsaron kasa da kasa, da ka’idoji masu ruwa da tsaki, tare da bayyana muhimman manufofin yin hadin gwiwa da tsarin dandali.
A yayin taron dandalin tattaunawar da aka gudanar yau da safe, mai taken “Shawarar tsaron kasa da kasa: Dabarun kasar Sin na daidaita matsalolin tsaro”, Qin Gang, ministan harkokin wajen kasar Sin ya ce, takardar ta nuna aniyar kasar Sin na kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsaron kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta gudanar da harkoki masu nasaba tsakanin manyan jami’ai a lokacin da ya dace, inda sassa daban daban za su tattauna kan batun tsaro.
Ministan ya yi nuni da cewa, takardar ta kunshi fannoni guda 20 da za a mai da hankali kan yin hadin gwiwa a kai, ciki had da goyon bayan MDD wajen jagorantar daidaita harkokin tsaro, kara kokarin taimakawa juna da mu’amala da juna tsakanin manyan kasashe, yin kira ga manyan kasashe da su ba da jagora wajen aiwatar da doka da yin zaman daidai wa daida da hada kai, nuna adawa da yin danniya da cin zalin wasu, da sa kaimi kan yin tattaunawa don warware batutuwan dake jawo hankali sosai cikin lumana. (Tasallah Yuan)