A yau Alhamis, kasar Sin ta sanar da kakaba takunkumai kan kamfanoni 3 masu alaka da rundunar sojin Amurka da wasu manyan jami’ansu 10, don gane da batun sayarwa yankin Taiwan makamai.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, ta ruwaito kamfanonin 3 sun hada da Edge Autonomy Operations LLC da Huntingdon Ingalls Industries Inc. da kuma Skydio Inc.
- Xi Ya Mika Gaisuwar Ban Girma Ga Dattawa A Jajibirin Ranar Tsofaffin Kasar Sin
- Asirin Amurka A Fannin Tada “Yakin Hakkin Dan Adam” A Duniya
Sanarwar ta kara da cewa, an kuma kakaba takunkumi kan kadarori da arzikin kamfanonin 3 da mutanen 10 wadanda za a iya dauka da ma wadanda ba za a iya ba, dake cikin kasar Sin.
Haka kuma, za a haramtawa dukkan hukumomi da kamfanoni da daidaikun mutanen kasar Sin mu’amala ta kudi ko hadin gwiwa da sauran ayyuka da wadancan mutane da kamfanoni.
Bugu da kari, za a hanawa mutanen 10 Visa ko shiga kasar Sin, ciki har da yankunan musammam na Hong Kong da Macao. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp