Kasar Sin ta yi nasarar samar da wani tsari mai cin kilogiram 100 na ruwan Hydrogen wanda ya kunshi tanki da bututu da sauransu, da ake dorawa manyan motocin dakon kaya masu amfani da makamashin Hydrogen.
A cewar kamfanin kula da harkokin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin, wanda ya kirkiro wannan tsari, a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwa da manyan motocin dakon kaya masu amfani da makamashin Hydrogen ke bukata, sabon tsarin wanda aka samar da shi a kasar Sin zai taimakawa manyan motocin dakon kaya wajen inganta tafiyar sama da kilomita 1,000 idan suka yi caji sau 1.
- Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa
- Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Inganta Dukkanin Matakan Samar Da Ci Gaba Ta Hanyar Kirkire-Kirkire
Idan aka kwatanta da na baya wanda suke da kusan girma daya, sabon tsarin zai iya cin karin kaso 20 na ruwan Hydrogen tare da rage kaso 30 na kudin da ake kashewa.
A cewar wani masani na kamfanin, bisa la’akari da yadda zai iya daukar kilogiram 100 na ruwan Hydrogen, wannan tsari ya kai matsayin na kasa da kasa a fannin inganci da adana sinadarin Hydrogen da lokacin da ake bukata na sake zubawa sinadarin. (Fa’iza)