Kasar Sin za ta ci gaba da amfani da wasu manufofin kudi 3, ciki har da tsarin bayar da izinin fitar da wani adadi na hayakin carbon, yayin da ake kokarin jagorantar cibiyoyin hada-hadar kudi wajen karfafa bada goyon baya ga raya muhalli da sauran bangarori.
Wata sanarwar da babban bankin kasar ya fitar, ta ce za a tsawaita tsarin bayar da izinin domin taimakawa rage fitar da hayaki mai guba zuwa karshen shekarar 2024, inda aka sanya wasu cibiyoyi na cikin gida da na ketare cikin tsarin, domin zurfafa hadin gwiwa kan bangaren hada-hadar kudi mai kiyaye muhalli.
A cewar bankin, za a aiwatar da tsari na musamman domin inganta amfani da kwal ta amintacciyar hanya mafi dacewa a karshen bana domin karfafa komawa ga makamashi mai tsafta da cimma burin kai wa matsayin koli na fitar da hayaki mai guba da abubuwan dake iya zuke su.
Babban bankin zai kuma tsawaita tsarin musamman na bayar da rance ga bangarorin jigila da na sufuri har zuwa karshen watan Yunin bana, domin karfafa taimakon kudi ga ayyukan sufuri da na jigilar kayayyaki.
A mataki na gaba kuma, bankin ya yi alkawarin ci gaba da kara tallafawa dunkulewar hada-hadar kudi da raya muhalli da kirkire-kirkiren kimiyya da ginin ababen more rayuwa da sauran wasu muhimman bangarori da karfafa manufofin kudi masu rauni. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp