Ma’aikatar kudi ta kasar Sin da ma’aikatar agajin gaggawa a yau Litinin sun kara ware wani kaso na tallafin agaji na yuan miliyan 400, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 56 a matsayin kudin agaji ga lardunan Gansu da Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin, inda aka fi mai da hankali kan sake tsugunar da jama’a da biyan diyya ga iyalan wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.2 da ta auku a makon da ya gabata. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp