Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga kasa da kasa, su karfafa hadin gwiwa wajen shawo kan fashin teku a yankin gabar tekun Guinea.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya, yayin zaman da Kwamitin Sulhu na MDD ya gudanar kan gabar ta tekun Guinea.
Jakadan na kasar Sin, ya ce ya kamata kasashen duniya su taimakawa kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika da takwararta ta kasashen tsakiyar Afrika, da hukumar kula da gabar tekun Guinea da sauran kungiyoyi da hukumomin shiyyoyi, wajen taka muhimmiyar rawa domin karfafa ayyukan yaki da fashin teku.
Ya ce a shekarun baya-bayan nan, an gayyaci sojojin ruwa na kasar Sin, su gudanar da atisayen yaki da fashin teku da takwarorinsu na Nijeriya da Kamaru da sauran wasu kasashe, haka kuma an samar da kayayyakin aiki a matsayin tallafi ga kasashen dake gabar teku.
Har ila yau, cikin watan Mayun bana, sojojin kasar Sin sun gudanar da wani taron karawa juna sani kan yanayin tsaro a yankin gabar tekun Guinea, inda ta cimma wata muhimmiyar yarjejeniya da kasashen yankin.
Bugu da kari, Geng Shuang, ya ce a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da musaya da kasashen dake gabar teku a fannonin tsaro da ayyukan ‘yan sanda da sojoji da sauran wasu bangarori da fadada hadin gwiwa a aikace da taka rawa wajen bayar da karin gudunmuwa ga tsaron gabar tekun Guinea. (Fa’iza Mustapha)