Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, ya kamata a yi duk mai yiwuwa, wajen ganin an shawo kan illar da al’umma ke fuskanta a kasashen Rasha da Ukraine, yana mai jaddada cewa, ya kamata dukkan bangarorin da abin ya shafa su ba da cikakkiyar kariya ga fararen hula, da gine-ginen jama’a.
Game da nazarin da kwamitin sulhu ya yi kan batun jin kai a kasar Ukraine, Geng Shuang ya ce, a wannan zamanin da ake ciki na dunkulewar duniya, aiwatar da cikakkun takunkuman da ba su ware kowa ba, na kara saurin watsuwar rikici ne kawai, da kara daga farashin kayayyaki masu yawa a duniya, da kuma kawo cikas ga jerin sana’o’i a tsakanin kasa da kasa, da sanya kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa su fuskanci kalubale.
A cewarsa, ya kamata kasashen duniya su hada kai don ba da kariya, ga gudanar kasuwannin abinci, da makamashi, da hada-hadar kudi yadda ya kamata, da kawar da cikas a fannin siyasa, yayin da ake gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa.
Baya ga haka, ya jaddada cewa, ya kamata a kiyaye fararen hula da gine-ginen jama’a, kuma kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su samar da sauki, wajen kwashe mutane da ba da agajin jin kai.
Ya ce, bin hanyar lumana babbar dabara ce ta warware rikicin jin kai na Ukraine, kuma ita ce hanyar daya tilo ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro cikin dogon lokaci a kasar da ma shiyyar baki daya.
A matsayinta na kasa mai daukar nauyi, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar gani, wajen inganta shawarwarin zaman lafiya, da ba da gudummawa mai kyau wajen kawar da matsalolin jin kai. (Mai fassara: Bilkisu)